Tinubu Ya Nada Tsohon Shugaban PDP Shirgegen Mukami Bayan Mutuwar Mai Rike da Kujerar
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Ambasada Desmond Akawor a matsayin sabon kwamishinan Tarayya
- Tinubu ya nada Akawor a matsayin kwamishinan hukumar RMAFC mai wakiltar jihar Ribas bayan mutuwar wakili a jihar
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangare yada labarai, Ajuri Ngelale a yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Ambasada Desmond Akawor a matsayin kwamishinan Tarayya daga jihar Ribas.
Tinubu ya nada Akawor ne a matsayin kwamishinan Tarayya na Hukumar Rarraba Kudaden Shiga (RMAFE), Legit ta tattaro.
Yaushe Tinubu ya yi sabon nadin na Akawor?
Shugaban ya yi wannan nadin ne a yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba inda sabon kwamishinan zai kama aiki bayan Majalisar Dattawa ta tantance shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya sanar a shafin Twitter a yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba.
Sanrawar ta ce sabon kwamishinan wanda ke wakiltar jihar Ribas zai maye gurbin marigayi tsohon kwamishina daga jihar.
Wasu mukamai Akawor ya rike a Najeriya?
Marigayin Honarabul Asondu Wenah Templeya rasu a farkon wannan wata da muke ciki ta Nuwamba, Tribune ta tattaro.
Kafin nadin Akawor shi ne daraktan kamfe na Ministan Abuja, Nyesom Wike yayin da ya ke neman zarcewa a shekarar 2019.
Ya kuma rike shugaban jam'iyyar PDP a jihar Ribas a shekarar 2020 bayan rike mukamin ambasada a kasar Korea ta Kudu.
Ma'aikata dubu 5 za su rasa albashin Disamba
A wani labarin, akalla ma'aikatan Gwamnatin Tarayya dubu biyar ne ba za su samu albashin watan Disamba mai kamawa ba.
Shugaban manyan ma'aikatan Gwamnatin Tarayya shi ya bayyana inda ya ce su na kokarin shawo kan matsalar da gaggawa inda ya ce matsalar takardu ne ya shafe su.
Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke fama da matsanancin hali saboda tsadar rayuwa da talauci tun bayan cire tallafin mai da Bola Tinubu ya yi.
Asali: Legit.ng