APC vs PDP: Kotun Ɗaukaka Kara Ta Kori Ɗan Majalisa, Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zaɓe

APC vs PDP: Kotun Ɗaukaka Kara Ta Kori Ɗan Majalisa, Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zaɓe

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ɗan majalisar PDP, ta ayyana APC a matsayin wacce ta samu nasara a zaben mamban majalisar dokokin Ogun
  • Kotun ta bayyana cewa ta gamsu da hujjojin cewa ɗan takarar PDP, Owodunni ya janye daga takara a mazabar mamba mai wakiltar Ikenne
  • Ta umarci INEC ta baiwa Kunle Sobukola na jam'iyyar APC shaidar lashe zaben ɗan majalisar dokokin Ogun na mazaɓar Ikenne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a jihar Legas ta rushe nasarar Babajide Owoduni, mamba mai wakiltar mazaɓar Ikenne a majalisar dokokin jihar Ogun.

Kotun ta kori ɗan majalisar jihar wanda ya ci zaɓe karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abubuwa 2 na sani yayin da kotun daukaka kara ke yanke hukunci kan soke zaben gwamnan Nasarawa

Kotu ta kori ɗan majalisar PDP na jihar Enugu.
Kotun daukaka kara ta kori dan majalisar Jam'iyyar PDP na jihar Ogun Hoto: punchng
Asali: UGC

Bayan nan Kotun ɗaukaka karar ta ayyana Kunle Sobukola na jam'iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓe a mazaɓar Ikenne ta jihar Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yanke wannan hukunci ne a ƙarar da aka ɗaukaka zuwa gabanta mai lamba CA/1B/EP/SHA/OG/23/2023.

Kotun ta umarci hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bai wa ɗan takarar APC, Sobukola, shaidar lashe zaɓe a matsayin zabaɓɓen ɗan majalisa mai wakiltar Ikenne a majalisar dokokin Ogun.

Dalilin tsige ɗan majalisar jiha na PDP

A watan Maris, 2023, INEC ta ayyana Owodunni, ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya samu nasara duk da a ranar 6 ga watan Maris ya sanar da ficewa daga PDP.

An tattaro cewa kwana 12 gabanin zabe, Owodunni, ya fice daga PDP kuma ya jange daga takara a wata wasiƙa da ya aike wa jam'iyyar da kuma INEC.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnoni 3, Kotun daukaka kara ta tsaida ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan APC

Owodunni ya kuma garzaya babbar kotun jihar Ogun, inda ya yi rantsuwa cewa ya janye daga takara a zaben 18 ga watan Maris.

A lokacin da PDP ta samu sakon matakin da ya ɗauka, ta yi kokarin sauya ɗan takara amma INEC ta ƙi yarda kuma ta tabbatar da Owodunni a matsayin ɗan takarar da ta sani.

A kotun sauraron karrakin zsɓe, Owodunni ya ba da labarin yadda aka yi garkuwa da shi tare da tilasta masa sanya hannu kan takardar janyewa daga takara.

Sai dai ƙaramar kotun ta tabbatar masa nasarar da ya samu bisa hujjar cewa ya janye daga takara ƙasa da kwanaki 90 gabanin zaɓe, don haka ba ta halarta ba.

Amma kotun ɗaukaka ƙara ta amince da waɗannan hujjoji kana ta jingine hukuncin kotun zaɓe, ta soke nasarar PDP.

Gwamna Uzodinma Ya Dakatar da Kwamishina

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Imo ya dakatar da kwamishinan filaye, bincike da tsare-tsare, Honorabul Noble Atulegwu, daga muƙaminsa nan take

Ya kuma dakatar da mai ba gwamna shawara kuma babban manajan hukumar gidaje ta jihar, Mbakwe Obi Jnr, ya umarci su bar ofis

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262