Zaben Gwamnan Kano: Kotun Koli Za Ta Warware Rudanin Da Aka Samu a Kotun Daukaka Kara, NNPP

Zaben Gwamnan Kano: Kotun Koli Za Ta Warware Rudanin Da Aka Samu a Kotun Daukaka Kara, NNPP

  • Jam'iyyar NNPP ta ce tana fatan Kotun Koli ta kawo karshen wannan dambarwar da ta mamaye hukuncin Kotun Daukaka Kara kan zaben jihar Kano
  • Jam'iyyar ta yi mamakin yadda takardun CTC suka nuna Gwamna Abba shi ya lashe zaben, amma kotu ta fadi akasin hakan a ranar Juma'a
  • Da wannan ta ke ganin akwai makarkashiya kan hukuncin kotun, lamarin da jam'iyyar ta kira abin dariya da izgili ga Kotun Daukaka karar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Kakakin jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya bayyana cewa za a magance cece-kucen da ake tafkawa dangane da CTC na hukuncin Kotun Daukaka Kara kan rikicin zaben gwamnan jihar Kano a Kotun Koli.

Kara karanta wannan

Yanzu yanzu: Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan zaben Gwamna Sule na Nasarawa

Kotun Daukaka Kara ta amince da hukuncin da kotun kararrakin zabe ta Kano ta yanke na korar Gwamna Abba tare da bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.

Gwamna Abba na jihar Kano
Jam'iyyar NNPP ta ce Kotun Koli ce kawai za ta iya warware wannan rudani da ya mamaye hukuncin Kotun Daukaka Kara Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Kwamitin alkalai uku na kotun daukaka kara ya yi watsi da karar da Gwamna Yusuf ya shigar bisa hujjar da ta shafi matsayinsa mamba a jam’iyyar NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharhin hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke

Sai da an shiga rudani a ranar Talata yayin da wani sashe na takardar CTC ta hukuncin kotun, ya bayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaben.

A jawabin hukuncin da ya gabatar, Mai Shari'a Moore Adumein ya karanto daga shafi na 68 cewa:

"wannan kotun ta ba wanda ake kara na farko nasara tare da yin watsi da wannan karar, saboda gaza samun hujjojin da za su tabbatar da zargin da mai karar ke yi."

Kara karanta wannan

NNPP ta aika sako ga NJC kan hukuncin kotun daukaka kara na korar Gwamna Abba na Kano

Da ya ke tsokaci kan lamarin a gidan talabijin na Arise tv, kakakin NNPP ya bayyana dambarwar da ta mamaye takardun shari'ar matsayin abin dariya da zama aibi ga kotun, Daily Trust ta ruwaito.

NNPP ta zargi akwai makarkashiya a hukuncin kotun

"A ce kotu ta yanke hukunci ranar Juma'a amma ta ki bayar da takardun hukuncin har sai bayan kwana biyar, ai daga ji kasan akwai wata a kasa."
"Ko ma dai menene, hakan ya nuna karara akwai zamba a lamarin nan, wannan wata dambarwa ce da muke kallon ta mamaye fanni shari'a."

- Ladipo Johnson

Channels TV ta ruwaito gwamnatin jihar Kano na zargin cewa akwai wata makarkashiya a batun takardun hukuncin kotun amma dole Kotun Koli ce za ta iya magance matsalar.

Kotun Daukaka Kara ta yi martani kan takardar CTC

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta magantu kan takarar hukuncin shari'ar gwamnan Kano da ta yanke, wanda wani sashe ya nuna akasin sakamakon hukuncin kotun

Babban magatakardar kotun, Umar Bangari, ya ce an samu kuskuren rubuta takardar ne, amma za a gyara idan bangarorin biyu sun bukaci hakan, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.