Kano: Alkalai 'Yan Adam Ne Ba Ma'asumai Ba, APC Ta Fadi Yadda Za a Gyara Bayan Fitar CTC
- Yayin da ake cece-kuce kan fitar da takardun CTC, jami'yyar APC ta ce wannan kuskure ne na dan Adam taka
- Jam'iyyar ta bayyana cewa a matsayinsu na 'yan Adam, alkalan ba su fi karfin yin kuskure ba wanda za a iya gyara wa
- Mai bai wa jam'iyyar shawara a bangaren shari'a, Abdul Adamu shi ya bayyana haka a yau Alhamis Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jami'yyar APC ta bayyana cewa alkalai mutane ne kamar kowa don haka za su iya yin kuskure.
Jam'iyyar ta ce kuskure ne aka samu yayin fitar da takardun CTC da ake ta cece-kuce a kai wanda hakan ke nuna su 'yan Adam ne, cewar Channels TV.
Mene APC ke cewa kan takardun CTC?
Yayin da ya ke kare kuskuren, Abdul Adamu mai bai wa jam'iyyar shawara a bangaren shari'a, ya ce kuskuren ya tabbatar da cewa su ma mutane ne kamar kowa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce babu wanda ya fi karfin kuskure a cikin mutane kuma tabbas kuskure aka yi yayin fitar da takardun CTC da ya bai wa Abba Kabir nasara.
Wannan cece-kuce na zuwa ne bayan fitar da takardun CTC da ke dauke da bayanai da su ka bambanta da na hukuncin kotu, cewar Arise TV.
Abdul ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba.
Wane dama su ke da shi na yin gyara?
Ya ce:
"Kotun koli ta fitar da sanarwa inda ta ce alkalai mutane ne ma su yin kuskure, 'yan Adam ne su.
"Za su iya yin kuskure ko su kara ko rage wani abu, dole za su iya yin kuskure yayin alkalancinsu."
Adamu ya kara da cewa dokar kasa ta ba su dama da ikon gyara idan an samu irin wannan kuskuren.
APC, Abba Kabir sun ja daga kan zanga-zanga
A wani labarin, Gwamnatin jihar Kano ta halasta zanga-zangar da aka gudanar a jihar bayan fitar da takardun CTC a ranar Talata.
Wannan na zuwa ne bayan jami'yyar APC ta yi Allah wadai da zanga-zangar da cewa an yi ta ne don tayar da hankulan mutane.
Asali: Legit.ng