Kano: Abba Kabir, APC Sun Ja Layi Kan Zanga-zangar da Aka Gudanar Bayan Fitar da Takardun CTC

Kano: Abba Kabir, APC Sun Ja Layi Kan Zanga-zangar da Aka Gudanar Bayan Fitar da Takardun CTC

  • Gwamnatin jihar Kano ta barranta da jami'yyar APC kan zanga-zangar da ta barke a jihar kan hukuncin kotun daukaka kara
  • A jiya Laraba ce mutane su ka fito zanga-zanga don nuna fushinsu bayan fitar da takardun CTC da ya bambanta da hukuncin da aka yanke
  • Jam'iyya APC na zargin NNPP da tunzura jama'a don ta da hankula a birnin tare da kone-kone kan hukuncin kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya barranta da jami'yyar APC kan zanga-zangar da ake yi a jihar.

A jiya Laraba ce zanga-zanga ta barke bayan kotun daukaka kara ta saki takardun CTC da ya bai wa Abba Kabir nasara a kotu.

Kara karanta wannan

Kano: Takardar CTC ta nuna Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Yusuf, Femi Falana

Gwamna Abba Kabir na Kano da APC sun ja layi kan zanga-zangar da aka gudanar a jihar
Hukuncin kotu ya jawo rigima a jihar Kano. Hoto: Abdullahi Ganduje, Abba Kabir.
Asali: Facebook

Mene Abba Kabir ya ce kan zanga-zangar a Kano?

Atoni Janar kuma kwamishinan Shari'a a jihar, Haruna Isa Dederi ya ce zanga-zanga ta inganta ganin yadda aka sauya hukuncin shari'ar a kotun daukaka kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dederi ya bayyana haka ne a yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba yayin hira da manema labarai.

Ya ce Allah ne kadai ya san abin da zai faru ganin yadda aka yanke hukuncin da ya ci karo da juna, Vanguard ta tattaro.

Ya ce:

"Wannan zanga-zangar ta halasta, ina mai tabbatar muku Allah ne kadai ya san abin da zai faru game da wannan hukuncin kotu.
"Mutane ba su ji dadin yadda abubuwa ke tafiya ba, su na cikin bakin ciki, mu na fatan zaman lafiya amma ba za mu iya dakatar da su ba.
"Mutane ba su nuna rashin amincewarsu ba a hukuncin karamar kotun amma yanzu sun fito saboda jita-jitar da su ke samu kan hukuncin."

Kara karanta wannan

NNPP ta aika sako ga NJC kan hukuncin kotun daukaka kara na korar Gwamna Abba na Kano

Mene martanin APC kan zanga-zangar a Kano?

A martaninshi, Abdul Adamu, mai bai wa APC a jihar Kano shawara a bangaren shari'a ya ce ba su amince da wannan zanga-zangar ba.

Ya ce zanga-zangar da aka aminta da ita a doka ita ce wacce aka gudanar cikin lumana, cewar Channels TV.

Ya ce:

"APC ba ta daukar wannan zanga-zangar a matsayin ta lumana, mun gano mutane na kona taya da kuma rike da makamai."

Adamu ya zargi jami'yyar NNPP ta ingiza mutane don yin zanga-zangar tashin hankali inda ya ce ya na da muryar da aka nada a matsayin shaida.

Zanga-zanga ta barke a jihar Kano

A wani labarin, bayan fitar da takardun CTC a ranar Talata, zanga-zanga ta barke a jihar Kano kan hukuncin kotu.

Mutane da dama sun fito zanga-zangar ce don nuna rashin amincewarsu kan hukuncin kotun daukaka kara a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.