APC Ta Yi Watsi da Takardar CTC Da Ke Tabbatar da Abba a Matsayin Gwamnan Kano: “Kuskure Ne”
- Jam'iyyar APC ta kalubalanci sahihancin takardar CTC da ke tabbatar da Abba Yusuf a matsayin gwamnan Kano
- Da yake magana kan hukuncin CTC masu karo, mai ba APC shawara kan harkokin shari'a ya yi ikirarin cewa kuskure ne da za a gyara
- Jam'iyyar mai mulki ta dage cewa ba sabon abu bane samun kuskure a hukuncin kotu kuma ana iya gyarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Farfesa Abdulkarim Kanna, mai ba jam'iyyar APC shawara kan harkokin shari'a, ya yi martani ga kwafin takardar CTC na kotun daukaka kara da ke yawo.
APC ta dage cewa hukuncin kotu ya ayyana Gawuna a matsayin mai nasara, cewa an yi kuskure a CTC
Ya bayyana cewa takardar CTC da ke tabbatar da zaben Abba Kabir Yusuf na NNPP, a matsayin zababben gwamnan jihar Kano "kuskure ne".
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Kanna, ya yi karin hasken ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a Abuja a sakatariyar jam'iyyar na kasa, rahoton Daily Nigerian.
An samu rudani a jihar Kano a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, da fitowar kwafin takardar CTC, na hukuncin kotun daukaka karar kan zaben gwamnan jihar.
Sai dai kuma, Atoni Janar na jihar kuma kwamishinan shari'a, Haruna Isa-Dederi, ya yi korafi cewa takardar CTC din ya nuna cewa kotun daukaka karar ta tabbatar da nasarar Yusuf a zaben.
Da yake martani, mai ba APC shawara kan harkokin shari'a ya bayyana ci gaban a matsayin kuskuren rubutu da kotun za ta gyara.
"Sai dai kuma, mu da muke lauyoyi mun san cewa sau da yawa kurakuran rubutu suna faruwa a kwafin takardar hukunci na CTC.
“A ka’ida ba zai zama rudani ba idan da ace ba batun siyasa ba ne domin ba zai zama karo na farko da za a ga kurakuran rubutu irin wannan a cikin hukunci ba.
“Kuma a matsayinmu na lauyoyi, mun saba da irin wannan yanayi; abin da ake yi shi ne kawai a gyara wannan kuskuren. Abu mafi mahimmanci shi ne hukuncin da aka karanta a gaban kotu,” in ji Mista Kanna.
Ya kara da cewa irin wannan kuskuren rubutu ba sabon abu bane a tsarin kotu.
Kotu ta magantu kan shari'ar gwamnan Kano
A wani labarin, mun ji cewa babban magatakardar Kotun Daukaka Kara, Umar Bangari ya yi kawo karshen ce-ce-kucen da ake yi kan hukuncin da kotun ta yanke kan zaben gwamnan Kano.
Mista Bangari ya ce abin da aka gani a takardar da ta fitar na hukuncin shari'ar kuskure ne na wallafa wanda kuma bai karyata ko sauya sakamakon da kotun ta yanke ba.
Asali: Legit.ng