Kano: An Fada Wa Kotun Koli Wanda Za Ta Ayyana Ya Yi Nasara a Tsakanin Gwamna Abba da Nasiru Gawuna

Kano: An Fada Wa Kotun Koli Wanda Za Ta Ayyana Ya Yi Nasara a Tsakanin Gwamna Abba da Nasiru Gawuna

  • Gamayyar kungiyoyin farar hula da masu rajin tabbatar da dimokuradiyya 100 sun soki hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
  • A ranar Juma'a 17 ga watan Nuwamba, kotun ta tsige Gwamna Abba tare da ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen
  • Gamayyar ƙungiyoyin ta ce hukuncin ya saɓawa tsarin dimokuraɗiyyar da aka kafa Najeriya a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gamayyar ƙungiyoyin farar hula 100 da masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya, sun buƙaci kotun ƙolin ƙasar nan da ta tabbatar da zaɓin masu kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar Kano da ake taƙaddama a kai.

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Kano: Kotun daukaka kara ta bukaci lauyoyi su dawo da takardun hukuncin da ta yanke

Kotun ɗaukaka ƙara ta kori Gwamna Abba Yusuf na jam'iyyar NNPP daga muƙaminsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

An shawarci kotun koli kan shari'ar gwamnan Kano
Kotun daukaka kara ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba Hoto: Dr Nasir Yusuf Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gamayyar ƙungiyoyi ta yi fatali da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin ne bayan da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta tsige Yusuf a watan Satumba, inda ta ce jam’iyyar NNPP ta gaza tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar NNPP ta yi watsi da hukuncin inda ta ce tana kan hanyar zuwa kotun ƙoli.

Gabanin fara zaman kotun ƙolin, gamayyar ƙungiyoyin rajin kare dimokuradiyya sun yi kira ga kotun ƙolin ta yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara tare da dawo da nasarar da suka ce al'ummar Kano sun ba Gwamna Yusuf, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Kada ka yi barci": Gabanin hukuncin kotu, babban malamin addini ya gargadi dan takarar gwamnan PDP

Jaridar Blueprint ta ambato shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Francis Obinna, a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba yana cewa

"Kotun koli, a matsayinta na babbar kotu a ƙasar nan tana da alhakin tabbatar da adalci da tabbatar da bin doka da oda."
"Muna kira da a sake duba hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a shari’ar gwamnan Kano.”

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Fitar da Takardun CTC

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta fitar da takardun hukuncin da ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Kano.

Kotun ta fitar da takardun na CTC ne bayan an fara ƙorafin ta ƙi sakin takardun bayan ta yanke hukuncinta a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng