Bayan Tsige Gwamna, Shugaban Majalisar Dokoki da Mataimakinsa Sun Yi Murabus a Jihar Arewa

Bayan Tsige Gwamna, Shugaban Majalisar Dokoki da Mataimakinsa Sun Yi Murabus a Jihar Arewa

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Moses Thomas, da mataimakinsa, Gwottaon Fom, sun yi murabus daga muƙamansu
  • Jim kaɗan bayan haka mambobin majalisar suka zaɓi sabbin shugabannin da za su maye gurbinsu a majalisar
  • Sai dai ana hasashen wannan ci gaban ba zai rasa nasaba da hukuncin tsige Gwamna Celeb Mutfwanga da wasu ƴan majalisun PDP ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Shugaban majalisar dokokin jihar Filato, Honorabul Moses Thomas, ya yi murabus daga muƙaminsa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Haka nan kuma mataimakin shugaban majalisar dokokin, Honorabul Gwottaon Fom, ya bi sahunsa ya yi murabus daga kan kujerarsa mai lamba biyu a majalisar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ɗauki mataki mai tsauri yayin da rikici ya tsananta a majalisar dokokin jihar PDP

Shugaba da mataimakinsa sun yi murabus a majalisar dokokin jihar Filato.
Shugaban Majalisar Dokokin Filato da Mataimakinsa Sun Yi Murabus Hoto: dailytrust
Asali: UGC

An naɗa waɗanda zasu maye gurbinsu

Bayan sun ɗauki wannan matakin ne, ƴan majalisar suka zaɓi mamba mai wakiltar mazaɓar Pankshin ta arewa, Gabriel Dawang, a matsayin sabon shugaban majalisar dokokin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Honorabul Timothy Dantong mai wakiltar mazaɓar Riyom, shi aka zaɓa ya zama sabon mataimakin kakakin majalisar ta jihar Filato.

Me ya kawo wannan sauyin?

An tattaro cewa wannan sauyin da aka samu lokaci ɗaya ba zai rasa nasaba da matakin kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamna Caleb Mutfwang da wasu ƴan majalisar PDP ba.

A ranar Lahadin da ta gabata, kwamitin alkalai uku na Kotuj ɗaukaka ƙara, ya rushe nasarar Gwamna Mutfwang tare da ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya ci zaɓe.

Kotun ta yanke cewa Gwamnan bai cancanci tsayawa takara ba saboda bai samu halastaccen ɗaukar nauyi daga PDP ba kasancewar ba ta da tsari ingantance.

Kara karanta wannan

Yanzu: An samu sabon Kakakin Majalisa da Mataimakinsa a Filato

Bisa haka ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bai wa ɗan takarar APC shaidar zama zabaɓben Gwamna a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watam Maris, 2023.

Majalisar dattawa ta naɗa sabon shugaban marasa rinjaye

A wani rahoton na daban kuma Sanata Abba Moro na PDP daga jihar Benuwai ya zama sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya.

Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da naɗin tsohon ministan, wanda zai maye gurbin Sanatan Filato da kotu ta tsige.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262