Yanzun nan: Atiku Abubakar Ya Maida Martani Mai Zafi Kan Tsige Gwamnonin Arewa Biyu
- Alhaji Atiku Abubakar ya yi Alla wadai da hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara na tsige wasu gwamnonin jam'iyyar adawa
- Atiku, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya zargi APC mai mulki da gurgunta tsagin adawa da kuma jefa dimokuradiyya cikin hadari a kasa
- A cewar Atiku, idan APC ba ta yi nasara ta hanyar magudi ba, tana amfani da kotu wajen karbe jihohin da ‘yan adawa ke mulki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya maida martani kan tsige gwamnonin jam'iyyarsa biyu.
A makon jiya, Kotun ɗaukaka ƙara ta soke nasarar Gwamna Celeb Nutfwang na jihar Filato da takwarasan gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, duk mambobin PDP.
Yayin da Kotun ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Filato, ta bada umarnin sake zaɓe a kananan hukumomi huɗu a Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya maida martani kan hukuncin tsige gwamnonin PDP
Da yake mayar da martani ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, 2023, tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya zargi APC da yi wa ƴan adawa ƙarfa-ƙarfar kwace mulki.
Atiku ya faɗi haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Abdulrasheed Shehu, ya wallafa a manhajar X wadda aka fi sani da Twitter.
Haka nan kuma Atiku ya zargi jam'iyya mai mulki da kokarin murƙushe adawa gaba ɗaya, inda ya ƙara da cewa kyaun demokuraɗiyya shi ne barin kowa ya yi ra'ayinsa.
A sanarwan mai taken, "Ajendar APC na kwace haƙƙin jam'iyyun adawa," Atiku ya yi zargin cewa APC ta gurgunta ƙarfin adawa ta hanyar maguɗin zaɓe ko kwace a Kotu.
Ya ce:
“Abin da ya fi daukar hankali shi ne cewa duk jihohin da kotun ta yanke hukunci mai cike da ruɗani jam’iyyun adawa ne ke iko da su."
Sabuwar Rigima Ta Ɓalle a Hedkwatar Jam'iyyar PDP
A wani rahoton na daban Sabuwar matsala ta kunno kai yayin da masu zanga-zanga suka mamaye hedkwatar jam'iyyar PDP a Abuja.
Gungun masu zanga-zangar sun nemi dukkan mambobin kwamitin gudanarwa NWC na ƙasa su yi murabus.
Asali: Legit.ng