Akwai Matsala: Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Tsige Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa
- Hankali ya karkata ga kotuna yayin da fusatattun ƴan takarar gwamna da jam’iyyun da suka fafata a zaɓukan 2023 ke jiran hukunci
- Masu shigar da ƙara na neman a yi musu adalci domin ganin sun cimma burinsu na samun ɗarewa kujerar gwamna
- Da yake magana kan rikicin zaɓen gwamna da ba a warware ba a jihar Adamawa, Primate Elijah Ayodele ya ce ya hango gwamna Ahmadu Fintiri zai ci gaba da mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Yola, jihar Adamawa - Primate Babatunde Elijah Ayodele a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, ya ce manyan kotuna a Najeriya ba za su iya korar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ba.
Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, da ke Legas, ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
'Ba za ku iya ƙwace kujerar Fintiri ba', Ayodele ga APC
Malamin ya bayyana cewa babu wata Kotun ɗaukaka ƙara ko kotun ƙoli da za ta iya tsige gwamnan na jihar Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fintiri babban jigo ne a babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.
Primate Ayodele ya bayyana hakan ne a wani faifan da ya sanya a X inda yake cewa:
"Babu wata kotun ɗaukaka ƙara ko kotun ƙoli da za ta iya tsige gwamnan Adamawa, sai dai kotun Allah, amma da wannan mata (Aisha Binani), kawai ɓata lokaci ne, ɓata dukiyarta, ɓata sanin yin abin da ya kamata."
"Don haka, yin wata huɓɓasa domin cimma hakan ba zai taimaka ko kaɗan ba."
A ƙarshen watan Oktoba ne kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Adamawa ta tabbatar da sake zaben Fintiri a zaɓaɓɓen gwamnan jihar a zaɓen gwamna na watan Maris na 2023.
Kotun mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Theodora Uloho ta yi fatali da bukatar ƴar takarar gwamna a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Aisha Binani Dahiru saboda rashin cancanta.
Bayan haka, jam'iyyar APC ta ƙi aminceea da hukuncin kotun zaɓen, inda ta garzaya zuwa kotun ɗaukaka ƙara.
Ayodele Ya Hango Nasarar Gwamna Uzodinma
A wani labarin kuma, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya hango nasarar Gwamna Hope Uzodinma na APC a zaɓen gwamnan jihar Imo.
Babban faston ya bayyana cewa ya hango jam'iyyar APC ta doke abokan hamayyarta a zaɓen gwamnan na jihar Imo.
Asali: Legit.ng