Zaben Gwamnan Bayelsa, Imo da Kogi: Dalilai 4 da Suka Sa 'Yan Takarar Labour Party Shan Kaye

Zaben Gwamnan Bayelsa, Imo da Kogi: Dalilai 4 da Suka Sa 'Yan Takarar Labour Party Shan Kaye

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Zaɓen gwamna na jihohin Kogi, Imo da Bayelsa ya zo har ya wuce, amma ƴan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) ba su yi abin kirki ba.

Yayin da hankali ke kan ƴan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP), ana sa ran ƴan takarar jam'iyyar LP za su taɓuka wani abu, amma hakan bai faru ba.

Dalilin rashin nasarar 'yan takarar LP a zaben Imo, Bayelsa da Kogi
'Yan takarar LP ba su yi abun kirki ba a zaben gwamnan Imo, Bayelsa da Kogi Hoto: Athan Nneji Achonu/Udengs Eradiri/BARR, OKEME'2023
Asali: Facebook

A cikin wannan rahoton, Legit.ng za ta yi tsokaci kan abubuwan da suka haddasa kayar da ƴan takarar jam'iyyar LP.

Rashin Peter Obi

A lokacin babban zaɓen shekarar 2023 a watan Fabrairu da Maris, ƴan takarar jam’iyyar LP da dama sun amfana da cewa Peter Obi ya tsaya takara kuma da shi za a yi zaɓe.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamnan Imo: Ɗan takarar LP Achonu ya bayyana matsayarsa kan batun amincewa da shan kaye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai soyayya da fatan alheri daga ƴan Najeriya ta yadda mafi yawan ƴan takarar jam’iyyar LP suka yi amfani da hakan suka ci zaɓensu.

Sai dai, ba haka lamarin ya kasance ba a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, kowane ɗan takara sai ya yi gwagwarmayar neman ƙuri’u, domin yin amfani da Peter Obi domin cin zaɓe ba zai yiwu ba.

Rashin ƙwaƙwazo a soshiyal midiya

Tafiyar magoya bayan Peter Obi wacce aka fi sani da 'Obidients' ta yi suna sosai a lokacin babban zaɓen 2023.

Magoya bayan Obi sun mamaye dandalin sada zumunta kuma ba sa jin kunyar bayyana ra'ayoyinsu.

Jam'iyyar Labour Party da ƴan takararta sun samu shahara a X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), Facebook da sauransu.

Ƴan takarar jam'iyyar LP a Imo, Bayelsa da Imo

Ƴan takarar da jam’iyyar Labour Party ta gabatar a lokacin zaɓen ba su da wani tagomashi in banda Sanata Athan Achonu a jihar Imo.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan kujerar sakatarenta na kasa

A jihar Bayelsa, ɗan takarar jam'iyyar LP, Injiniya Udengs Eradiri, tsohon shugaban majalisar matasan Ijaw kuma kwamishinan cigaban matasa a shekarar 2018, ya kasa samun ƙuri’u dubu a ƙananan hukumomi takwas na jihar.

Hakan take a wajen ɗan takarar LP na jihar Kogi, Okeme Adejoh, wanda shi ma bai yi abun a zo a gani ba.

Sanata Achonu shine ɗan takara ɗaya tilo da ke da alaƙa da jama’a.

Rarrabuwar kai

Rarrabuwar kai ya kasance wani abin da ya kai ga rashin nasara ga jam'iyyar LP a zaɓen gwamnonin da aka yi.

A jihar Kogi, wani ɓangare na jam’iyyar ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye kimanin mako guda kafin zaɓen.

Lamarin dai bai banbanta a jihar Imo ba, domin ɓangaren Lamidi-Apapa sun maka Achonu kotu domin hana shi tsayawa takara.

Achonu ya fito ne daga ɓangaren Julius Abure yayin da bangaren Apapa ya samar da Ukaegbu Joseph.

Kara karanta wannan

Sabuwar guguwa ta tunkaro Ganduje da APC gabanin zaɓen 2027

Dalilan Nasarar APC a Zaɓen Kogi

A wani labarin kuma, mun tattaro muku dalilan da suka sanya jam'iyyar APC da ɗan takararta Ahmed Usman Ododo suka lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi.

Ƙarfin mulki da siyasar ƙabilanci da aka yi a jihar na daga cikin dalilan da suka sanya jam'iyyar lallasa abokan adawarta a zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng