PDP v APC: Halin da Ake Ciki a Plateau Yayin da Kotun Daukaka Kara Ke Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna

PDP v APC: Halin da Ake Ciki a Plateau Yayin da Kotun Daukaka Kara Ke Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna

  • Kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Plateau a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba
  • Garin Jos na fuskantar tsauraran matakan tsaro a wurare daban-daban gabanin hukuncin na kotun ɗaukaka ƙara
  • Ɗan takarar gwamna a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Nentawe Yilwatda Goshwe, ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar nasarar Gwamna Caleb Mutfwang

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jos, Jihar Plateau - An girke jami'an tsaro a wurare daban-daban a Jos, babban birnin jihar Plateau, gabanin yanke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kan zaɓen gwamnan jihar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, sojoji ɗauke da makamai sun killace wurare daban-daban ciki har da harabar kotun ɗaukaka ƙara da ke kan titin Yakubu Gowon da ke Jos.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da ke neman tsige gwamnan PDP a Arewa

An baza jami'an tsaro a Plateau
An baza jami'an tsaro a Plateau yayin da kotun daukaka kara ke yanke hukunci Hoto: Caleb Mutfwang/@Chikaskumle
Asali: UGC

An tattaro cewa sojojin sun ajiye tankunansu masu sulke a gaban harabar kotun ɗaukaka ƙara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ɗaukaka kara za ta yanke hukunci kan ƙarar zaɓen gwamnan jihar Plateau a yau Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.

Meyasa aka girke jami'an tsaron?

Kakakin Rundunar Sojin, Kyaftin Oya James, ya bayyana cewa an tsaurara matakan tsaro ne domin hana karya doka da oda.

"Kun san halin da ake ciki a garin saboda hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke. Don haka, akwai fargaba a garin domin kotu za ta yanke hukunci a ranar Lahadi. Kuma kun san mun yi namijin ƙoƙari wajen ganin mun dawo da zaman lafiya a Plateau. Don haka, a irin wannan yanayi, duk da cewa aikin na ƴan sanda ne, amma jami'an mu suna nan ne kawai su sa ido domin kada mu koma inda muka baro, domin hana karya doka da oda."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana matakin dauka na gaba bayan kotun daukaka kara ta tsige shi

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wasu mazauna birnin Jos waɗanda suka bayyana yadda jama'a suka gudanar da harkokinsu a cikin birnin a yau.

Malam Bashir ya bayyana cewa a yau da safe mutane sun fito gudanar da harkokinsu amma zuwa wajen ƙarfe 12:00 na rana, sawu ya ɗauke inda mutane ba su sake fitowa ba sai gab da lokacin da kotun ta yanke hukuncinta.

Ziya'ul Dauda ya bayyana cewa a unguwarsu ba a girke jami'an tsaro ba inda mutane suka yi ta gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.

Malamin Addini Ya Gargadi Gwamna Mutfwang

A wani labarin kuma, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya aike da gargaɗi ga gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yin kotun ɗaukaka ƙara ke shirin yanke hukunci.

Primate Ayodele ya ce gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang "yana bukatar addu'a" idan yana fatan hana kotun daukaka kara ta tsige shi daga kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel