"Alhakin Rusau Ne" Shugaban Jam'iyya Na Kano Ya Maida Martani Kan Tsige Abba Gida-Gida
- Abdullahi Abbas ya sadaukar da nasarar da APC ta samu a Kotun ɗaukaka ƙara ga mutanen da rusau na Gwamnatin Abba ya shafa a Kano
- Shugaban APC na jihar Kano ya ce tsige Abba Gida-Gida a karo na biyu ya nuna cewa dama tun farko Gawuna ne ya ci zaɓe
- Ya ƙara da cewa suna da ƙwarin guiwar sake samun nasara a Kotun ƙoli duba da kwararan hujjojin da suke da su a hannu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana farin cikinsa da hukuncin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf a Kotun ɗaukaka ƙara.
Abbas ya bayyana wannan nasara a matsayin nasarar ɗaukacin mazauna Kano musamman waɗanda rusau ɗin gwamnati mai ci ya shafa, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Idan baku manta ba, kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin Kotun zaɓe, wadda ta ayyana Nasiru Gawuna na APC a matsayin gwamnan Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani a wata hira da ya yi ranar Asabar a Kano, Abdullahi Abbas, ya ce wannan nasarar alama ce da ke nuna dama APC ce ta ci zaɓe tun farko.
Shugaban APC ya ce:
"Ina mai farin cikin sanar da dukkan mutanen da rusau na gwamnatin NNPP ya taɓa a filin idi, Salanta da sauran wurare cewa wannan nasarar ta ku ce, wanda zai cece ku ya iso."
"Muna tabbatar wa mutanen Kano cewa gwamnatinsu ta dawo, don haka babu sauran abin tsoro."
Mu ke da nasara har Kotun koli - Abbas
Bayan haka Abdullahi Abbas ya yi kira ga ɗaukacin magoya bayan jam'iyyar APC da su ci gaba da harkokin gabansu cikin kwanciyar hankali su guji shiga rigima ko tada yamutsi.
Da yake tsokaci kan yunkurin NNPP na zarcewa zuwa Kotun ƙoli, shugaban APC ta Kano ya ce suna da kwarin guiwar zasu ƙara samun nasara duba da hujjojin da suke da su a ƙasa.
Jagoran NNPP Ya Maida Zazzafan Martani
A wani rahoton kuma Jagora kuma wanda ya kafa jam'iyyar NNPP ya maida martani kan hukuncin tsige Abba Gida-Gida da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi.
Dakta Boniface Aniebonam, ya bayyana cewa babu mai hurumin kalubalantar zaman Abba mamban NNPP sai ɗan jam'iyya.
Asali: Legit.ng