Hukuncin Kano da Zamfara: APC Ta Yi Martani Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Abba Gida Gida

Hukuncin Kano da Zamfara: APC Ta Yi Martani Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Abba Gida Gida

  • Jam'iyyar APC ta yaba ma kotun daukaka kara kan tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ta yi
  • Jam'iyyar mai mulki ta ce hukuncin ya sake dawo da kwarin gwiwar mutane cewa kotuna sune hanyar samun adalci
  • An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya fitar a ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta mayar da martani kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tsige gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano tare da ayyana zaben gwamnan jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta tsige gwamnan Filato, alkalai sun ce APC ta ci zaben 2023

Sakataren labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya yaba da hukuncin da kotun ta yanke a cikin wata sanarwa da ya fitar.

APC ta yaba da hukuncin kotun daukaka kara kan zaben gwamnonin Kano da Zamfara
Hukuncin Kano da Zamfara: APC Ta Yi Martani Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Abba Gida Gida Hoto: Nasir Gawuna/Bello Matawalle
Asali: Facebook

Morka ya yabawa kotun daukaka karar kan tabbatar da hukuncin kotun zabe da ta bayyana Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar, a ranar 18 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar mai mulki ta yabawa bangaren shari’a kan jajircewar da suka nuna tare da karfafa musu gwiwa da su ci gaba da yin watsi da bita da kulli da barazana.

A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @OfficialAPCNg, APC ta ce hukuncin sun sake dawo da kwarin gwiwar mutane na cewa kotuna ne hanyar samun adalci.

"Gaba daya hukunce-hukuncen biyu suna nuna fa'ida da yancin kan bangaren shari'a, kuma sun sake dawo da kwarin gwiwar cewa kotuna, kuma sune ginshikin fatan samun adalci a kowani tsarin damokradiyya."

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun daukaka kara: Farfesan arewa ya yi gargadi kan yiwuwar barkewar rikici a Kano

Wani jigon APC, Aliyu Yusuf, ya shaida wa Legit Hausa cewa sun yi murna da waɗannan matakai da Kotu ta ɗauka a jihohin biyu domin zai ƙara wa jam'iyyar ƙarfi.

Malam Yusuf, ɗan asalin jihar Katsina ya ce:

"Idan muka karɓi waɗannan jihohin ƙarfin APC zai ƙaru a Arewa maso Yamma, kuma kowa ya san muhimmancin ƙuri'un yankin a zaɓe. Kuma dama tuni muka fara shirin tunkarar zaɓen 2027."

A cewarsa, masu suka da zagin shugaban ƙasa kan wannan hukuncin ba su san me doka ta ƙunsa ba, "Ita kotu tana duba hujjojin da ke gabanta ne ta yi hukunci."

Kano: Ministar Tinubu ta taya Gawuna murna

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa Mariya Mahmoud, karamar ministar babban birnin tarayya, ta nuna farin cikinta da hukuncin kotun daukaka kara wacce ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

A cewar Mariya, "Mun dade muna addu'a akan wannan hukunci". Ministar ta yi godiya ga Allah kan hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng