Tashin Hankali: Halin da Mutane Suka Shiga a Jihar Kano Bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tsige Abba
- Iyaye sun shiga tashin hankali da rashin tabbas bayan Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Rahotanni sun bayyana cewa iyaye sun garzaya makarantu sun ɗauko 'ya'yansu domin gudun abinda ka iya biyo baya
- Tun a jiya Alhamis, mutane suka fara zaman ɗar-ɗar bayan Kotun ta tsaida ranar raba gardama kan zaben gwamnan Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - An shiga tshin hankali a jihar Kano ranar Juma'a yayin da iyaye da masu kula da yara suka yi gaggawar zuwa ɗauko 'ya'yansu a makarantu.
Wani shugaban makarantun kuɗi a unguwar Normandsland da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano ya shaida wa Daily Trust yadda iyaye suka shiga damuwa.
Halin da iyaye suka shiga bayan yanke hukunci
A cewarsa, iyaye sun shiga fargabar cewa za a iya samun tashin-tashina a birnin sakamakon hukuncin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa mazauna Kano sun shiga yanayin ɗar-ɗar tun ranar Alhamis (jiya) lokacin da Kotun ɗaukaka ƙara ta tsaida Jumu'a a matsayin ranar yanke hukunci.
Bayan da kotun ta bayyana hakan a ranar Alhamis, mutane suka fara saye-sayen firgici, yayin da suke fargabar yiwuwar a sanya dokar hana fita a faɗin jihar.
Wani ɗan kasuwa a kasuwar Kantin Kwari, Yunusa Abdullahi, ya ce:
"Muna addu'a Allah ya sa abubuwa su tafi cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata matsala ba amma ni a karan kaina, ba zan fito kasuwa ba saboda ba wanda ya san abinda zai faru."
"Ina mamakin meyasa haka ke faruwa, kowa zai kwanta da wannan tunanin a zuciyarsa. Ka ga gobe duk yadda kuke ganin tituna cike da mutane zasu zama ba kowa."
"Kowa zai zauna a gida ba wanda zai fito saboda mun ga abinda ya faru lokacin da Kotun zaɓe ta yanke hukunci."
A tasa mahangar, wani ɗan kasuwa mai suna, Usman Bello, ya ce:
"Su yi abin da ransu ke so amma su sani cewa Allah yana kallo kuma sun sanya tashin hankali da fargaba a zuƙatan ɗumbin mutane, ba gaira babu dalili."
Yayin da Legit Hausa ta yi hira da wasu mazauna Kano, sun ce a ɓangarensu babu wani abu makamancin haka da ya faru, kowa na hidimarsa cikin kwanciyar hankali.
Abdulrasheed Abdullah, ɗan kasuwa a cikin Kano ya faɗa wa wakilin mu cewa ba abinda suka bari, sun fita kasuwa kuma su kansu masu saye sun fito.
Ɗan kasuwan ya ce:
"Gaskiya dai mun ci kasuwa, kawai dai zaka ga ko a kasuwa ne ana tattauta hukuncin da aka yanke, amma hakan bai hana mu harkokin gabanmu."
Dangane da batun iyaye kuwa, Malam Sanusi, ya ce babu wanda ya zo ɗaukar yara kafin lokacin tashi a makarantarsu da ke Hotoro.
Ya. ce idan ma hakan ta faru sai dai a wasu Unguwannin domin Kano na da faɗi, ba zai ƙaryata ba kai tsaye.
Abubuwan da suka sa Kotu ta tsige Abba Gida-Gida
Kuna da labarin Muhimman dalilin biyu Kotun ɗaukaka kara ta dogara da su wajen tsige Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan jihar Kano.
Ƙotun ta tabbatar da hukuncin Kotun zaɓe wacce ta sauke Abba daga mulki bayan soke halascin ƙuri'u 165,663 daga cikin ƙuri'unsa.
Asali: Legit.ng