INEC Ta Mika Satifiket Ga Sabon Gwamnan APC, Ya Tura Muhimmin Sako
- Hukumar INEC ta mika satifiket ga sabon zababben gwamna a jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo
- Hukumar ta mika satifiket din ne ga Ododo a birnin Lokoja na jihar Kogi a yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba
- Wannan na zuwa ne bayan Ododo ya yi nasara a zaben da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Hukumar zabe ta INEC ta mika satifiket ga zababben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo da mataimakinsa.
Hukumar zaben ta mika satifiket din ne a hedikwatarta da ke Lokoja a yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba, cewar Tribune.
Yaushe Ododo ya lashe zaben gwamnan Kogi?
Ododo na jam'iyyar APC ya samu nasara a zaben da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba da kuri'u 446,237.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da Murtala Ajaka na jam'iyyar SDP ya zo na biyu da kuri'u 259,052 sai kuma Dino Melaye na PDP da kuri'u 46,362.
Jim kadan bayan karbar satifiket din, Ododo ya yi wa 'yan jihar alkawarin ci gaba da ayyukan alkairi na Gwamna Yahaya Bello.
Wane martani 'yan takarar ke cewa kan zaben?
Ya godewa 'yan jihar kan irin goyon baya da su ka ba shi a lokacin zabe inda ya sha alwashin saka musu da ayyuka nagari a jihar.
Ya kuma godewa Gwamna Yahaya Bello da ya ba shi wannan dama na kasancewa gwamna a jihar, cewar Pulse.
Dan tararar jami'yyar SDP, Murtala Ajaka ya ce an tafka mummuna n magudi a zaben amma ba zai bata lokacinsa wurin kai kara kotun zabe.
Hukumar INEC ta ayyana Ododo wanda ya lashe zaben Kogi
A wani labarin, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ya ayyana Usman Ododo ba matsayin wanda ya lashe zaben Kogi.
Usman Ododo na jam'iyyar APC ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Ododo ya yi nasara kan dan takarar SDP, Murtala Ajaka da kuma dan takarar jam'iyyar PDP, Dino Melaye wanda ya zo na uku a zaben.
Asali: Legit.ng