Gaskiya Ta Fito: Manyan Dalilai 2 Da Suka Sa Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Gwamna Abba Na Kano
- Muhimman dalilin biyu Kotun ɗaukaka kara ta dogara da su wajen tsige Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan jihar Kano
- Ƙotun ta tabbatar da hukuncin Kotun zaɓe wacce ta sauke Abba daga mulki bayan soke halascin ƙuri'u 165,663 daga cikin ƙuri'unsa
- Sai dai ita kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke cewa gwamnan wanda aka tsige bai cancanta ya tsaya takara ba a lokacin da aka yi zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - A yau Jumu'a, 17 ga watan Nuwamba, 2023 Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a birnin tarayya Abuja ta sauke Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan jihar Kano.
Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar Nasir Gawuna na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
PDP vs APC: Halin da ake ciki a Plateau yayin da kotun daukaka kara ke yanke hukunci kan zaben gwamna
A rahoton da jaridar Arise tv ta haɗa, dalilai biyu suka sa Kotun ta tsige Gwamna Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Haramtattun ƙuri'u 165,663
Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe wanda ya tsige Gwamna Yusuf bayan soke halascin kuri'u 165,663 daga cikin ƙuri'un da ya samu.
Idan baku manta ba kotun zaɓen ta yanke wannan hukunci na soke ƙuri'un ne saboda, "Babu sutanfi da sa hannun hukumar zaɓe ta ƙasa INEC a jikin ƙuri'un."
2. Abba Kabir Yusuf bau cancanta ya tsaya takara ba
Bugu da ƙari, kotun ɗaukaka ƙaran ta kuma yanke hukuncin cewa Gwamna Yusuf bai cancanta ya tsaya takarar gwamna ba tun da farko sabida bai zama cikakken ɗan NNPP ba.
A cewar alkalan Kotun, tsigaggen gwamnan bai zama cikakken mamban NNPP ba kamar yadda doka ta tanada a lokacin da aka gudanar da zaɓen a watan Maris.
A rahoton Daily Trust, mai shari'a Adumein ya ce:
"Kamar yadda aka gano, Yusuf Abba bai zama mamban NNPP a lokacin da aka ce jam’iyyar ta dauki nauyinsa ba kuma bai cancanta ya tsaya takarar gwamnan jihar a watan Maris ba."
Martanin Yan Najeriya Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Abba
A wani rahoton na daban Jim kaɗan bayan Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da tsige Abba, yan Najeriya sun yi radda kan wannan batun.
Legit Hausa ta tattaro muku martanin mutane kan hukuncin, ciki harda hadimin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, watau Bashir Ahmad.
Asali: Legit.ng