Abba vs Gawuna: Malami Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru Bayan Kotu Ta Sauke Gwamnan Kano
- Yayin da ake ci gaba da yanke hukuncin shari'ar zaben jihar Kano, Fasto ya yi hasashen abin da zai faru a shari'ar
- Fasto Elijah Ayodele ya ce ya hango APC sun gama shirya kwace kujerar Abba karfi da yaji ko da a kotun koli ne
- Wannan na zuwa ne yayin da ake yanke hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar Kano a yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Shahararren Fasto ya bayyana abin da zai faru a shari'ar zaben gwamnan jihar Kano da ake yi yau.
Fasto Elijah Ayodele wanda shi ne shugaban cocin Evangelical Spiritual ya ce APC ta shirya kwace kujerar gwamnan Kano, Legit ta tattaro.
Mene Faston ke cewa kan shari'ar Kano?
Ayodele ya bayyana haka ne a yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba a shafinsa na Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya yi hasashen cewa shari'ar za ta kai har kotun koli idan aka yanke hukuncin kotun daukaka kara.
Ya ce:
"A hukuncin kotun da za a yi yau Juma'a a jihar Kano tsakanin Abba da Gawuna, na hango APC ta shirya kwace mulki a kotun ko kuma kotun gaba."
Wane hukunci kotun ta yanke a Kano?
Wannan na zuwa ne yayin da ake yanke hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar Kano a yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba.
Kotun ta kwace kujerar Abba Kabir na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a Kano.
Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe.
Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotun zabe a Kano
A wani labarin, shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya yi martani kan shari'ar zaben Kano da aka yanke a yau.
Ganduje ya ce ya na da tabbacin za su sake yin nasara a kotun koli da za a sake haduwa.
Wannan na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.
Asali: Legit.ng