Matasa Sun Yi Wa Gwamnan APC Ruwan Jifa da Ihu a Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Matasa Sun Yi Wa Gwamnan APC Ruwan Jifa da Ihu a Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamnatin jihar Benue ta karyata rahoton da ke yawo cewa matasa sun jefi Gwamna Alia yayin da ya kai ziyara wata kwaleji a Makurdi
  • Sakataren watsa labaran Gwamnan, Sir Kula Tersoo, ya bayyana rahoton da ƙarya wacce aka kirkira da nufin ɓata wa gwamnan suna
  • Ya kuma buƙaci yan jarida da su riƙa tabbatar da ingancin majiyoyin labarai kafin su wallafa a kafafensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Gwamnatin jihar Benuwai ta musanta rahoton da ke yawo a soshiyal midiya cewa wasu matasa sun jefi Gwamna Hyacinth Alia tare yi masa ihu a Makurdi.

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia.
Gwamnatin Benue Ya Musanta Rahoton Matasa Sun Yi Wa Gwamna Alia Ihu da Jifa Hoto: Gov Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Gwamnatin ta bayyana cewa rahoton wanda ya yi ikirarin cewa yayin ziyarar da Gwamna Alia ya kai kwalejin Vaatia a Makurɗi, wasu matasa cikin fushi sun masa ihu harda jifansa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

Sakataren watsa labaran Gwamnan, Sir Kula Tersoo, ya bayyana rahoton da ƙanzon kurege, mara tushe a wata sanarwa ranar Alhamis, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta bayyana rahoton a matsayin, "Ƙarya ne, tatsuniya, yaudara, kuma da yiwuwar an tsara shi domin wulakanci, da ɓatawa Gwamna Hyacinth Alia suna da jefa shi cikin yanayi."

Me ya faru yayin ziyarar Gwamna Alia?

Ta ce Gwamna Alia ya kai ziyara kwalejin ne bayan samun rahoton fashi a cikin gida, sata da kuma ɓarna a harabar makarantar.

Sakataren watsa labaran ya ƙara da bayanin cewa Gwamnan ya je ziyarar kuma ya kammala ya dawo cikin aminci ba tare da wani tada yamutsi ko bore ba.

Ya ce Gwamna Alia na da kyakkyawar alaƙa da al'umma da sahalewar yawo lungu da saƙo da kasuwannin jihar Benuwai cikin walwala ba tare da tsangwama ba.

Kara karanta wannan

Tirƙashi: Yadda yaro ɗan shekara 9 ya yi garkuwa da ƴar shekara 5 a Bauchi

Da yake hira da ƴan jarida, Tersoo ya bukace su da su rika bin ka’idojin aikin jarida da da’a, yana mai jaddada muhimmancin tantance majiyoyin labarai kafin wallafa su.

Ya ce:

“Wannan rahoton ba shi da tushe a takaice. Mu koyi yin bincike kuma a ko da yaushe mu tabbatar da gaskiyar duk wani rahoton da muka bayar.”

Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin shugaban NCC?

A wani rahoton na daban kuma Majalisar dattawan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da naɗin sabon shugaban hukumar NCC, Aminu Maida.

Hakan ya biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin sadarwa na majalisar a zaman ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262