Peter Obi Ya Caccaki Tinubu Kan Cewa Babu Kudi a Kasa, Ya Gaya Masa Abin da Ya Kamata Ya Yi

Peter Obi Ya Caccaki Tinubu Kan Cewa Babu Kudi a Kasa, Ya Gaya Masa Abin da Ya Kamata Ya Yi

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party ya caccaki Shugaba Tinubu kan cewa ya gaji basussuka a wajen magabatansa
  • Peter Obi ya yi nuni da cewa wannan wani salon kawo uzuri ne wanda gwamnatocin APC suka saba kawowa
  • Ya buƙaci Tinubu da ya bayyana yawan abin da ya gada domin ƴan Najeriya su san matsayar da ƙasar ta ke a ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya caccaki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu kan ikirarin da ta yi na gadon basussuka a hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a kwanakin baya.

A ranar Litinin din da ta gabata ne mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ƙasar na cikin taɓarɓarewar al’amura saboda bashin da ta gada.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana tarin gwaramar da shugabannin da suka gabacesa suka bar wa gwamnatinsa

Peter Obi ya caccaki Tinubu
Peter Obi ya soki Tinubu kan cewa babu kudi a kasa Hoto: Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A yayin wani taro da masu zuba jari a ƙasar Saudiyya a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, Tinubu ya bayyana cewa ya gaji basussuka daga shugabannin da suka gabace shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake mayar da martani a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) Obi ya ce kawo uzuri ya zama ruwan dare a wajen jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Tsohon gwamnan na Anambra ya ce Buhari ya yi irin wannan zargin a lokacin da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya miƙa masa mulki a shekarar 2015.

Obi ya jaddada cewa abin da gwamnatin APC ta rasa shi ne gaskiya da riƙon amana.

Wani ɓangare na rubutun na cewa:

"A jiya na karanta wani labari da ake yaɗawa daga gwamnatin tarayya ta yanzu a ƙarƙashin jam'iyyar APC cewa sun gaji ƙasa mai fatara daga gwamnatin APC da ta gabace su. Amma labarin ya ƙasa bayyana abin da suka gada wanda ya sanya muka samu fatara."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bai wa asibiti gudunmawar naira miliyan 20, ya bayyana dalili

"Ɗaya daga cikin manyan alhakin shugabanci shine nuna gaskiya da riƙon amana. Hakan na buƙatar gwamnati ta bayyana ainihin adadin giɓin da suka gada. Ya kamata a bayyana abin da aka gada domin jama’a su san inda muke da kuma inda muka dosa."

Tsohon Shugaba a APC Ya Koka Kan Halin Tinubu

A wani labarin kuma, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa (Areqa maso Yamma), Salihu Lukman, ya koka kan halin Tinubu tun bayan da ya shiga Villa.

Slaihu Lukman ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba ya bari jagorori da sauran waɗanda taimaka wajen samun nasararsa, su gan shi domin bayar da shawarwari idan an yi ba daidai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng