Zaɓen Gwamnan Imo: Ɗan Takarar LP Achonu Ya Bayyana Matsayarsa Kan Batun Amincewa da Shan Kaye

Zaɓen Gwamnan Imo: Ɗan Takarar LP Achonu Ya Bayyana Matsayarsa Kan Batun Amincewa da Shan Kaye

  • Zaɓen gwamnan jihar Imo na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba ya zo ya wuce, amma ana cigaba cece-kuce har yanzu kan zaɓen
  • Rahotanni sun bayyana a yanar gizo cewa, daga ƙarshe dan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) Athan Achonu ya amince da shan kaye, inda ya ziyarci gwamna Hope Uzodimma
  • Rahotannin sun kuma yi iƙirarin cewa Achonu ya taya Uzodimma murnar nasarar da ya samu a zaɓen, sai dai ya fito fili ya musanta hakan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Owerri, jihar Imo - Nathan Nneji Achonu, ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen gwamnan jihar Imo da aka yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya kai ziyara tare da taya wanda ya lashe zaɓen, Hope Uzodimma murna.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan kujerar sakatarenta na kasa

A wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, ta bakin mai magana da yawunsa, Chibuikem Diala, Achonu ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, inda ya ce ziyarar ta Uzodimma wani fata wanda ba zai taɓa faruwa ba.

Achonu ya musanta ta ya Uzodimma murna
Nathan Achonu ya hakikance shi ya lashe zaben gwamnan Imo Hoto: Hope Uzodimma, Senator Athan Nneji Achonu
Asali: Facebook

LP ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen gwamnan Imo

Achonu ya bayyana labarin taya murnar a matsayin "aikin yara wanda ba a rubuta da kyau ba", cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Don kaucewa shakku, Sanata Achonu ya yi watsi da sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta bayyana, ya kuma yi kira da a sake duba shi tare da soke shi."
"Shi (Achonu) ya kuma yi taron manema labarai na haɗin gwiwa da Samuel Anyanwu, ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, kuma ya dage cewa dole ne a sake duba sakamakon zaɓen gwamnan ko kuma a soke shi, yana mai gargadin cewa idan har INEC ba ta yi hakan ba, jama’a za su iya yin tawaye."

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Obiano ya sauya sheƙa daga APGA zuwa APC? Gaskiya ta bayyana

Idan ba a manta ba dai Gwamna Uzodimma na jam'iyyar APC ya samu ƙuri’u 540,308 inda ya doke ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Samuel Anyanwu, wanda ya samu ƙuri'u 71,503 yayin da Achonu na LP, wanda ya zo na uku ya samu ƙuri'u 64,081.

Dalilin Shan Kashin LP da PDP a Zaɓen Imo

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Imo a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Hope Uzodimma, ta bayyana dalilin da ya sanya jam'iyyun PDP da LP suka sha kaye a zaɓen gwamnan jihar.

Gwamnatin ta yi nuni da cewa jam'iyyun ba su shirya ba domin dukkaninsu suna fama da rikice-rikicen cikin gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng