Dalilai 3 da Suka Sa Timipre Sylva Na APC Ya Sha Kaye a Zaben Gwamnan Bayelsa

Dalilai 3 da Suka Sa Timipre Sylva Na APC Ya Sha Kaye a Zaben Gwamnan Bayelsa

  • Wani bincike da Legit Hausa ta yi, ya gano wasu dalilai da ka iya zama silar shan kayen jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Bayelsa da ya gudana
  • Duk da kasancewar jam'iyyar ce mai mulki a kasa, sai dai hakan bai hana dan takarar gwamnan, Timipre Sylva shan kasa a hannun Douye Diri na PDP ba
  • Daga cikin dalilan da ka iya zama silar faduwar jam'iyyar, sun hada da rikicin cikin gida da ya mamaye jam'iyyar APC a matakin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yenagoa, Bayelsa - An gudanar da zaben gwamnan jihar Bayelsa na 2023 a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, zaben da ya ja hankulan 'yan Najeriya tare da bibiyar yadda ya gudana.

Kara karanta wannan

Zabe ya kammala a Kogi, INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe, ya fi kowa adadin kuri'u

Gwamna mai ci, Duoye Diri, ya sake tsayawa takara a zaben, karkashin jam'iyyar PDP kuma ya yi nasarar samun tazarce, bayan samun kuri’u 175,196.

Timipre Sylva, tsohon gwamnan jihar, wanda shine dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya zo na biyu da kuri’u 110,108.

Timipre Sylva
Daga cikin dalilan da ake ganin sun jawo faduwar Sylva, akwai zabar abokin takara Hoto: Timipre Sylva
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanne dalilai ne su ka haifar da faduwar Sylva a zaben? Legit.ng ta yi nazari.

1) Zabar abokin takara

Ga wasu 'yan Bayelsa, suna ganin kuskuren da ya jawo faduwar Sylva a zaben shi ne zabar abokin takararsa. Abokin takarar Sylva a zaben shine Joshua Miciver, tsohon shugaban masu fafutuka kuma tsohon dan fursuna.

A cewar wani rahoto na jaridar The Nation, Maciver ya samu shiga cikin fursunonin da marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua ya yi wa afuwa a shekarar 2009, tare da wasu tsagerun Neja Delta.

Kara karanta wannan

PDP ta lshe karamar hukuma ta farko yayin da INEC ta fara tattara sakamakon karshe a Bayelsa

2) Rikicin cikin gida na APC

Watakila, daya daga cikin manyan dalilan da ya sa Sylva ya fadi zaben shi ne rarrabuwar kawuna a jam'iyyarsa da kuma fada tsakanin shugabannin jam'iyyar na jihar.

Kafin zaben na ranar Asabar din da ta gabata, an samu rashin jituwa a tsakanin amintattun jam’iyyar da jiga-jigan jam’iyyar game da kayyakin da za su yi amfani da su a zaben.

Da yawa daga cikin shugabannin jam'iyyar sun fice daga jam'iyyar, suna nuna adawa da fitowar Sylva a matsayin wanda zai yi takara karkashin jam'iyyar. Kazalika, bai yi wani yunkurin sasantawa don dawo da su ba, inji jaridar This Day.

3) Goyon bayan da Diri ya samu daga Jonathan

Goyon bayan da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nuna wa Diri a karshen yakin neman zaben sa ya jawo karin masu jefa kuri'u ga gwamnan - maimakon Sylva.

Kamar kace an kwace kuri'un daga hannun Sylva an mika wa Diri, musamman a karamar hukumar Ogbia inda aka yi imanin cewa matakin Jonathan ya kawo cikas ga kokarin Samuel Ogbuku, shugaban hukumar raya Neja Delta (NDDC).

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da su ka taimaki APC, suka Kashe LP da PDP a zaben Gwamnan Imo

Gwamna Diri ya samu tazarce a Bayelsa

Douye Diri, gwamnan jihar Bayelsa kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, ya yi nasarar lashe zabe, wanda ya ba shi damar yin tazarce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.