Ka Canza Hali: Tsohon Shugaba a APC Ya Fadi Kuskuren Tinubu Daga Shiga Aso Rock

Ka Canza Hali: Tsohon Shugaba a APC Ya Fadi Kuskuren Tinubu Daga Shiga Aso Rock

  • Salihu Lukman ya zargi Bola Ahmed Tinubu da rufe kokar da magoya baya da ‘yan jam’iyya za su iya zama da shi
  • Tsohon mataimakin shugaban APC ya ce wannan salo da shugaban Najeriyan ya dauka za su hana fadan gaskiya
  • Lukman ya bukaci Tinubu ya bude kunnuwansa domin masu kishin kasa su rika ankarar da shi kan kura-kuransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya fara kokawa kan Bola Ahmed Tinubu.

A farkon makon nan Punch ta rahoto Alhaji Salihu Lukman ya na cewa jagorori da sauran masu ruwa da tsaki a APC ba su iya ganin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Abba v Gawuna: An Ja Hankalin Bola Tinubu Kan Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

Shugaban kasa
Shugaba Bola Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

‘Dan siyasar yace toshe kofa ga magoya baya da jagorori ba zai taimaki Bola Tinubu da APC ba, za a rasa masu nuna masa inda an yi ba daidai ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran na APC mai mulki ya yi wannan gargadi ne a wani jawabi da ya fitar a garin Abuja da nufin ya magance matsalolin cikin gidan jam’iyyarsu.

Jawabin Salihu Lukman a kan Tinubu

"Na farko, babbar matsalar da shugabannin APC su ke da ita da gwamnatin Tinubu ita ce rashin iya haduwa da shi.
Watakila saboda kalubalen da yake fuskanta na matsin lamba ne daga masu neman mukamai a cikin gwamnati.
Wannan zai iya zama gaskiya a lokuta da-dama, amma bai kamata ya zama an yi wa kowa da kowa shamaki ba."

- Salihu Lukman

Tinubu: Lukman ya ce akwai gyara a APC

Kara karanta wannan

Ododo: Mutum 4 a APC da Su ka Share Mani Hanya Aka Zabe Ni Gwamnan Jihar Kogi

Lukman ya ce a matsayin jam’iyyar da ke kaunar kawo cigaba, bai kamata a tafi a haka ba, Sahara Reporters ta fitar da wannan rahoto a makon nan.

A jawabin da ya fitar, Lukman ya ce ya kamata amintattun ‘yan APC su zama masu kisshin kasa, su yi kokari wajen ganin gwamnati ta cin ma nasara.

Da gaske 'Yan APC ba su ganin Tinubu?

Darektan yada labaran APC na kasa, Bala Ibrahim ya yi matukar mamaki da ya ji mutum irin tsohon shugaba a jam’iyya ya na irin wannan magana.

Kamar yadda shugaban kasa zai rika auna kokarin wadanda ya ba mukami, Lukman ya ce kyau shi ma ya dauki gyara idan dai ya yi kuskure a mulki.

Rabu da APC ko PDP – Gwamnan Bauchi

Duk da yana Shugaban Gwamnonin PDP, ana da labari Gwamnan jihar Bauchi watau Bala Mohammed ya ce Bola Tinubu zai gyara Najeriya a mulkinsa.

Yadda Bola Tinubu ya kawo cigaba iri-iri a Legas a shekarun baya, Gwamna Bala Mohammed ya ce haka gwamnatin tarayya za ta gyara kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng