Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamanan APC

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamanan APC

  • Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyar PDP ta shigar inda ta kalubalanci nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagas
  • Yayin yanke hukunci ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, kotun ta yi fatali da karar PDP da dan takararta bisa rashin cancanta, inda ta tabbatar da hukuncin kotun zabe
  • Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ayyana Sanwo-Olu da mataimakinsa, Dr. Obafemi Hamzat a matsayin wadanda suka lashe zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Lagos - Kotun daukaka kara da ke zama a Lagas, ta yanke hukunci a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, inda jam'iyyar APC mai mulki ta yi nasara, rahoton The Cable.

Kotun daukaka karar ta yi fatali da karar jam'iyyar PDP da dan takararta, Olajide Adediran, wanda ke kalubalantar nasarar Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe aben gwamna na ranar 18 ga watan Maris a jihar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta rantsar da sabon sanatan PDP da kotun daukaka kara ta bai wa nasara

Sanwo-Olu da Hamzat sun yi nasara a kotun daukaka kara
Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamanan APC Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Kotu ta yi fatali da karar PDP da dan takararta

Kwamitin kotun mai mutum uku ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Lagas wanda ya tabbatar da nasarar Babajide Sanwo-Olu a ranar 25 ga watan Satumba, jaridar The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya riki cewa wadanda suka shigar da kara sun gaza tabbatar da zarginsu na magudi da rashin cancantar Sanwo-Olu da mataimakinsa Dr. Obafemi Hamzat.

Alkalan sun ce:

"Duk da cewar duk batutuwan kafin zabe ne, masu kara (PDP da Adeniran) sun gaza tabbatar da su. Masu karar sun zo hannu goma sannan su tafi hannu haka siddan. Kawai dai sun ji dadin ranarsu a kotu. An yi fatali da kararsu."

Kotu ta tanadi hukunci a zaben Nasarawa

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta kawo cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, na APC ya shigar gabanta.

Kara karanta wannan

Yanzu yanzu: Kotun daukaka kara na shirin yanke hukunci a karar da ke neman tsige gwamnan APC

Gwamnan ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ɗaukaka ƙara yana kalubalantar mafi akasarin hukuncin Kotun zabe, wadda ta tsige shi daga matsayin Gwamnan Nasarawa.

Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓen Gwamnan Nasarawa ta sauke Sule kana da ayyana ɗan takarar PDP, David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓe, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng