Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matsayarta Kan Kujerar Sakararenta na Kasa

Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matsayarta Kan Kujerar Sakararenta na Kasa

  • Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar PDP ya yanke shawara kan kujerar sakataren jam'iyyar na ƙasa
  • Rigingimu dai sun dabaibaye wannan kujerar ne a lokacin da yake kanta ya zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamnan Imo da aka kammala
  • Sai dai, an matsa masa lamba kan ya yi murabus, inda NWC ta bayyana cewa babu wani sharaɗi a kundin tsarin mulkin jam’iyyar da ke tabbatar da cewa dole ne ya yi murabus

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya yanke shawarar dakatar da Hon. Sunday Kelly Ude Okoye a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

An yanke wannan hukuncin ne yayin wani taro da aka yi a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, inda aka jaddada cewa PDP na bin ƙa'idoji wajen zaɓar shugabanninta.

Kara karanta wannan

Sabuwar guguwa ta tunkaro Ganduje da APC gabanin zaɓen 2027

Anyanwu ya koma kujerarsa ta sakataren PDP
Bayan rashin nasara a zaben Imo, Anyanwu ya koma kujerarsa ta sakataren PDP na kasa Hoto: Samuel Anyanwu
Asali: Facebook

A wannan rana, Sanata Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamnan jihar Imo da a ka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, ya koma ofishinsa da ke sakatariyar jam'iyyar a Abuja inda aka tarbe shi cikin farin ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NWC ta bayyana cewa bai kamata Ude Okoye ya gabatar da kansa a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa ba, sannan ta bukaci dukkanin ɓangarorin da ke rigima a kotu kan kujerar da su janye ƙararsu, saboda bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Tun da farko dai NWC ta yi ƙarin haske kan cewa kujerar sakataren jam'iyyar na ƙasa akwai mai ita, kuma ba a buƙatar Sanata Anyanwu ya yi murabus domin shiga zaɓen gwamnan jihar Imo.

NWC ta bayyana cewa sanar da yin murabus da ke cikin kundin tsarin mulkin PDP ba ta shafi waɗanda ke neman mukamin siyasa ba, kuma dokar zaɓen da aka yi wa kwaskwarima a 2022 ba ta da tanadin murabus ɗin masu riƙe da muƙamai da za su fafata a zaɓe ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Obiano ya sauya sheƙa daga APGA zuwa APC? Gaskiya ta bayyana

Shugaban jam'iyyar PDP ya bayyana matsayarsa

Shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa Umar Illiya Damagum, ya bayyana cewa umarnin kotu da ke cin karo da juna a kan lamarin ya yi tasiri a kan hukuncin.

Duk da bayyana batun a matsayin na cikin gida, NWC ta umurci duk masu ƙara kan lamarin da su janye ƙararsu a kotu

A kalamansa:

"Na san za ku yi tambaya game da rikicin kujerar sakataren jam'iyya na ƙasa. Al’amarin cikin gida ne, kuma an warware shi."
"NWC ta umurci duk waɗanda suka yi ƙara da su koma su janye ƙararsu a Kotu. Ba zan bari a dame da umarnin kotu ba."

PDP Ta Yi Sabon Sakatare Na Ƙasa

A wani labarin kuma, jam'iyyar PDP ta sanar da naɗin Setonji Koshoedo a matsayin muƙaddashin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagum, wanda ya sanar da naɗin Setonji, ya bayyana cewa an naɗa shi ne na wucin gadi har zuwa lokacin da za a kammala shari'a kujerar a kotun Enugu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng