Sabuwar Guguwa Ta Tunkaro Ganduje da APC Gabanin Zaɓen 2027
- Shekara uku da kusan rabi kafin babban zaɓen 2023, sabuwar rigima ta kunno a jam'iyyar APC mai mulki
- Wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar sun koka kan yadda kuɗin siyan fom na tsayawa takara a 2027 za su yi tsadar gaske
- Sai dai, jam'iyyar ta yi nuni da cewa a kwantar da hankula a jira sai lokaci ya yi kafin su fara surutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Wata sabuwar guguwa ta kunno kai a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki kan tsadar kuɗin siyan fom ɗin tsayawa takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar.
Hakan dai ya biyo bayan yadda kuɗaɗen siyan fom na tsayawa takara ke cigaba da karuwa tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2014, cewar rahoton Daily Trust.
Kuɗin fom din takarar shugaban ƙasa da gwamnonin jam’iyyar APC a shekarar 2014, gabanin zaben 2015, ya kai Naira miliyan 27.5 da miliyan 5. A shekarar 2019, ya ƙaru zuwa Naira miliyan 45 da kuma Naira miliyan 22.5. Sai dai kuma, ya haura zuwa Naira miliyan 100 da miliyan 50 a shekarar 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An koka kan tsadar fom a APC
Sai dai, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, sun buƙaci shugabannin jam’iyyar APC da su rage kuɗin takarar a 2027, inda suka yi zargin cewa duk da an samu biliyoyin Naira daga sayar da fom ɗin tsayawa takara kafin zaɓen 2023, jam’iyyar ta kasa bada bayanin yadda aka kashe kuɗaɗen.
Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa (Arewa maso Yamma) Salihu Mohammed Lukman, a wata sanarwa da ya fitar, ya koka da yadda ake kara kashe kudaden da ake kashewa wajen tsayawa takara a jam’iyyar.
Lukman ya bayyana fargabar cewa nan da 2027, jam’iyyar APC za ta iya mayar da kuɗin fom Naira miliyan 250 domin tsayawa takarar shugaban ƙasa da naira miliyan 125 na takarar gwamna.
Wane martani jam'iyyar APC ta yi?
Amma sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce batun kuɗin fom na zaɓe mai zuwa duk hasashe ne.
Morka a wata tattaunawa ta wayar tarho ya bayyana cewa:
"An nemi a biya N1 ba yana nufin zai zama N2 a gaba ba. Yana iya zama kuma ana iya sanya wa ya yi ƙasa."
"Don haka dole ne mu jira har sai jam'iyyar ta yanke hukunci sannan mu mayar da martani. Don haka ba zan yi jayayya da Lukman a kan haka ba domin duk abin da yake faɗi hasashe ne."
Ganduje Ya Yi Magana Kan Nasarar APC a Imo da Kogi
A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan nasarar da jam'iyyar ta samu a zaɓen gwamnan jihohin Kogi da Imo.
Ganduje ya bayyana cewa nasarar ta nuna cewa al'umma sun gamsu da salon mulkin jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng