Tsohon Gwamna Obiano Ya Sauya Sheƙa Daga APGA Zuwa APC? Gaskiya Ta Bayyana

Tsohon Gwamna Obiano Ya Sauya Sheƙa Daga APGA Zuwa APC? Gaskiya Ta Bayyana

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya yi watsi da rahoton shirin sauya sheƙarsa zuwa jam'iyyar APC
  • Obiano ya nanata zamansa a jam’iyyar APGA, inda ya ƙara da cewa ya aminta da aƙidun jam'iyyar
  • Daga nan sai tsohon gwamnan ya yi kira ga wanda ya gaje shi, Charles Soludo, da ya cika alkawarin biyan hakkokin wadanda ya naɗa muƙamai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Awka, Anambra - Willie Obiano, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya musanta rahoton cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar APGA zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, shugaban jam'iyyar APC na jihar Anambra, Basil Ejidike, a baya ya ce tsohon gwamnan zai koma jam'iyyar nan ba da daɗewa ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bai wa asibiti gudunmawar naira miliyan 20, ya bayyana dalili

Obiano ya musanta komawa APC
Tsohon Gwamna Obiano ya musanta sauya sheƙa zuwa APC Hoto: Willie Obiano, Charles Soludo
Asali: Twitter

Amma mai magana da yawun tsohon gwamnan, Tony Nezianya, a wata sanarwa a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa sadaukarwa da biyayyar Obiano ga APGA ba ta taɓa zama cikin shakku ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nezianya ya ce tsohon gwamnan ya kasance mai fafutukar kare ƙa'idoji da aƙidun jam’iyyar APGA, “ya ​​yi aiki tuƙuru wajen inganta manufofinta,” ya kuma cigaba da tabbatar da nasarar jam’iyyar bayan ya bar ofis.

Daga nan sai ya fayyace cewa ba shi da wani shiri na ficewa daga jam’iyyar APGA, rahoton Businessday ya tabbatar.

Obiano ya nemi wata buƙata a wajen Gwamna Soludo

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Ba ni da wani shiri a yanzu ko nan gaba na ficewa daga jam’iyyar. Akwai jita-jita a cikin wani sashe na kafofin watsa labarai cewa na shirya sauya sheƙa."

Kara karanta wannan

Buhari ya aike da saƙo mai muhimmanci kan sakamakon zaɓen gwamnan jihohin Imo da Kogi

Daga nan ne Obiano ya yi kira ga gwamna Soludo na jihar Anambra da ya cika alƙawarin biyan alawus alawus ɗin sallamar dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da ya naɗa.

A cewar tsohon gwamnan, an yi alƙawarin ne a lokacin da zai bar gidan gwamnatin jihar.

Sanata Ifeanyi Ya Sauka Sheka Daga YPP Zuwa APC

A wani labarin kuma, Sanata Ifeanyi Ubah sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu ya sauya sheƙa daga jam'iyyar YPP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Sanatan ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauya sheƙar ne saboda rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar YPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng