Zaɓen Gwamnan Kogi: INEC Ta Bayyana Yadda Ta Samo Sakamakon Ƙarshe

Zaɓen Gwamnan Kogi: INEC Ta Bayyana Yadda Ta Samo Sakamakon Ƙarshe

  • Bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Kogi, hukumar zabe ta ƙasa ta bayyana yadda ta samo sakamakon ƙarshe
  • Idan dai za a iya tunawa hukumar zaɓe ta bayyana cewa za a sake gudanar da zaɓen a wasu sassan jihar
  • Sai dai hukumar zaɓen ta yi amfani da “yawan tazarar da ke tsakani” wajen tantance wanda ya lashe zaɓen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Lokoja, Kogi - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi amfani da “yawan tazarar da ke tsakani” domin tantance wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi na ranar 11, ga watan Nuwamba.

A cewar INEC, ta fasa gudanar da zaɓen cike gurbi na ranar 18 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Imo ta bayyana dalilin da ya sanya PDP, LP suka sha kaye a zaɓen gwamnan Imo

INEC ta fasa gudanar da zaɓen cike gurbi a Kogi
INEC ta yi amfani da tazarar da ke tsakani wajen bayyana wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kogi Hoto: Olukayode Jaiyeola
Asali: Getty Images

Haliru Sule, shugaban sashen wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a na ofishin INEC na jihar Kogi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Lokoja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Sule ya fayyace cewa, biyo bayan korafe-korafe daban-daban da aka samu yayin zaɓen na ranar Asabar, hukumar ta gudanar da bincike inda daga bisani ta sanar da sake gudanar da zaɓe a yankin Ogorimagongo da wasu ƙananan hukumomi.

A kalamansa:

"Amma lokacin da muka kalli duk abin da ake magana a kai, mun gano cewa ba mu da wani zaɓi da ya wuce yin amfani da tsarin tazarar da ke tsakani."
"Tsarin ya ce, idan adadin PVC da aka karɓa a rumfunan zaɓe, na inda ba a yi zaɓe ba ko kuma aka soke zaɓen, bai wuce tazarar da ke tsakanin wanda ya yi nasara da wanda ya faɗi ba, to hukumar za ta iya bayyana wanda ya lashe zaɓe."

Kara karanta wannan

Zaɓabben Gwamna Usman Ododo ya magantu kan nasararsa a zaɓen Kogi, ya durƙusa a gaban Yahaya Bello

"Kamar yadda yake a yanzu, babu wani zaɓen cike gurbi da za a yi a wata rumfar zaɓe a Kogi."
"Ta hakan, an kammala zaɓen gwamna a Kogi. Abin da ya rage shi ne ranar da za a bayar da takardar shaidar yin nasara ga wanda ya lashe zaɓen."

Sakamakon zaɓen da manyan ƴan takara suka samu

Da yake nuna godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki a zaɓen gwamnan Kogi, Sule ya bayyana cewa INEC ta bayyana Usman Ododo, ɗan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da ƙuri’u 446,237.

Murtala Ajaka na jam'iyyar Social Democratic Party, wanda ya zo na biyu ya samu ƙuri’u 259,052, yayin da Dino Melaye na jam'iyyar Peoples Democratic Party ya samu ƙuri’u 46,362.

Usman Ododo Ya Magantu Kan Nasararsa

A wani labarin kuma, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yi magana kan nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Ododo ya nuna godiyarsa ga Allah maɗaukakin Sarki kan wannan nasarar da ya ba shi a zaɓen, sannan ya godewa ubangidansa a siyasance Gwamna Yahaya Bello.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng