To Fa: Wakilin APC Ya Tubure, Ya Faɗi Abinda Ka Iya Canza Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Bayelsa

To Fa: Wakilin APC Ya Tubure, Ya Faɗi Abinda Ka Iya Canza Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Bayelsa

  • Wakilin APC a cibiyar tattara sakamakon zaɓen Gwamnan jihar Bayelsa, Dennis Otiotio, ya tubure ya ƙi sanya hannu a takardar sakamakon
  • Mista Otiotio ya yi haka ne domin nuna rashin gamsuwa da kuma zargin an soke ƙuri'u 80,000 na APC a wasu akwatunan zaɓe
  • A cewarsa, jam'iyyar APC ta ci zaben idan aka ƙara adadin kuri'un da aka soke a jimullar sakamakon zaɓen da INEC ta bayyana

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa - Wakilin jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Dennis Otiotio, ya ƙeƙashe ƙasa ya ƙi rattaba hannu a takardar sakamakon zaɓen Gwamnan jihar Bayelsa.

Dan takarar Gwamnan APC a jihar Bayelsa, Timipre Sylva.
Wakilin APC Ya Ki Sa Hannu Kan Takardar Sakamakon Zaben Gwamnan Bayelsa Hoto: Timipre Sylva
Asali: Facebook

Wakilin APC ya yi haka ne saboda yana zargin cewa an soke ƙuri'u 80,000 na jam'iyyarsa a wasu rumfunan zaɓe.

Kara karanta wannan

Hadimin Shugaba Tinubu ya magantu kan zaben Bayelsa, ya aike da sako ga gwamna Diri na PDP

Mista Otiotio ya yi wannan zargi ne yayin da kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ya nemi wakilan jam'iyyu su sa hannu kafin bayyana wanda ya ci zaɓe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta caccaki matakin soke kuri'u 80,000

Wakilin APC ya bayyana cewa ba za su lamurci soke ƙuri'u 80,000 ɗin da aka yi ba kan ƙa'ida ba, yana mai cewa ya kamata a yi amfani da ƙuri'un.

Ya kara da cewa jam'iyyar APC za ta rubuta wasiƙar neman sake nazari kan sakamkon zaɓen ta aika zuwa ga INEC.

Ya kuma nuna alamun cewa jam'iyyar ka iya shiga Kotu neman haƙƙinta idan INEC ya gaza ɗaukar matakin da ya dace kan wannan zargi.

APC ce ta lashe zaɓen Bayelsa in ji wakilinta

A cewar Otiotio, jam’iyyar APC ce ta lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa idan aka kara kuri’un da aka soke a cikin ƙuri'un jam'iyyar adawa ta jihar.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamnan Bayelsa: Gwamna Diri ya lashe zaɓe a ƙaramar hukumar da ta fi yawan ƙuri'u a Bayelsa

Sai dai fushinsa bai hana INEC bayyana Gwamna Douye Diri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar a jihar mai arzikin man fetur ba.

Ɗan majalisar PDP Ya Bai Wa Jami'an Tsaro Kayan Aiki

A wani rahoton kuma Honorabul Umar Yusuf yabo ya raba wa mutanen mazaɓarsa da hukumomin tsaro babura 200.

Ɗan majalisar tarayyan ya kuma bai wa mata 2,000 jarin Naira N50,000 kana ya raba wa wasu matan firiza don su fara sana'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262