Zaɓen Gwamnan Bayelsa: Gwamna Diri Ya Lashe Zaɓe a Ƙaramar Hukumar da Ta Fi Yawan Ƙuri'u a Bayelsa

Zaɓen Gwamnan Bayelsa: Gwamna Diri Ya Lashe Zaɓe a Ƙaramar Hukumar da Ta Fi Yawan Ƙuri'u a Bayelsa

  • Gwamnan jihar Bayelsa kuma ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar, Duoye Diri, ya sake lashe zaɓen wata ƙaramar hukuma
  • Gwamna Duoye Diri ya lashe zaɓen gwamna a ƙaramar hukumar Southern Ijaw, inda ya samu ƙuri'u 24,685
  • Abokin hamayyarsa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Timipre Sylva ya samu ƙuri'u 18,174 a ƙaramar hukumar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Gwamna Douye Diri ya lashe ƙaramar hukumar Southern Ijaw yayin da aka cigaba da tattara sakamakon zaben gwamnan Bayelsa a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamban 2023, cewar rahoton Channels tv.

Yayin da cibiyar tattara sakamakon zaɓen ta tafi hutu da misalin karfe 1:00 na rana, jami'in tattara sakamakon zaɓen na jihar Farfesa Faruq Kuta ya cigaba tattara sakamakon zaɓen da misalin karfe 2:20 na rana a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Hadimin Shugaba Tinubu ya magantu kan zaben Bayelsa, ya aike da sako ga gwamna Diri na PDP

Diri ya lallasa Sylva a Southern Ijaw
Gwamna Diri ya lallasa Timipre Sylva a ƙaramar hukumar Southern Ijaw Hoto: Timipre Sylva, Duoye Diri
Asali: Twitter

Diri ya lashe Southern Ijaw

Diri, ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen, ya samu ƙuri’u 24,685, inda ya doke abokin takararsa Timipre Sylva na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya samu ƙuri’u 18,174.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar Labour (LP) ta zo na uku da 119 daga cikin 50,153 da aka amince da su.

Sakamakon na baya-bayan nan na nufin Diri ya lashe ƙananan hukumomi shida cikin takwas na jihar mai arzikin man fetur yayin da Sylva ya samu biyu.

Sylva ya lashe zaɓen ƙaramar hukumar Brass da ƙuri'u 18,431 yayin da Diri na PDP ya samu ƙuri'u 12,602.

Jam'iyyar APC ta kuma samu nasara a ƙaramar hukumar Nembe inda ta samu ƙuri’u 22,248 yayin da Diri ya samu ƙuri'u 4,556.

Ga sakamakon zaɓen Southern Ijaw

Kara karanta wannan

To fa: Wakilin APC ya tubure, ya faɗi abin da ka iya canza sakamakon zaben Gwamnan jihar Bayelsa

APC - 18,174

LP - 119

PDP - 24,685

Timipre Sylva Ya Sake Lallasa Gwamna Diri

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya sake samun nasara a wata ƙaramar hukuma

Sylva ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar a ƙaramar hukumar Brass. Ɗan takarar gwamnan na APC ya fito ne daga ƙaramar hukumar Brass.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng