Sylva Vs Diri: Karamar Hukuma Ɗaya Tal da Zata Raba Gardama a Zaben Gwamnan Bayelsa Ta Bayyana

Sylva Vs Diri: Karamar Hukuma Ɗaya Tal da Zata Raba Gardama a Zaben Gwamnan Bayelsa Ta Bayyana

  • Ana hasashen ƙaramar hukuma ɗaya ce zata raba gardama a zaɓen Gwamnan jihar Bayelsa tsakanin APC da PDP
  • Zuwa yanzun INEC ta karɓi sakamakon kananan hukumomi 7 kuma Gwamna Diri na PDP ne ke kan gaba da tazarar ƙuri'u 58,577
  • Karamar hukumar Ijaw ta kudu tana da masu katin zaɓe 184,401 kuma yanki ne da APC ke da ƙarfi tun 2015

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Baylesa - Ijaw ta kudu, karamar hukumar da ke da masu katin zaɓe 184,401, ita ce ake hasashen zata yanke hukunci kan wanda zai lashe zaben gwamnan Bayelsa.

Timipre Sylva da Gwamna Douye Diri.
Karamar Hukuma Daya da Zata Yanke Wanda Zai Lashe Zaben Gwamna a Bayelsa Hoto: Timipre Sylva, Douye Diri
Asali: Facebook

Har yanzu dai ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma Gwamna mai ci a jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri ne a kan gaba da kuri'u mafi rinjaye.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Imo ta bayyana dalilin da ya sanya PDP, LP suka sha kaye a zaɓen gwamnan Imo

Gwamna Diri ya sha kashi hannu babban abokin hamayyarsa na APC, Timipre Sylva a sakamakon zaɓen karamar hukumar Brass da aka sanar ɗazu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sylva ya samu kuri'u 18,431 yayin da Diri ya samu kuri'u 12,602 a ƙaramar hukumar Brass, mahaifar ɗan takarar APC, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A jimullar sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta tattara kawo yanzu, Diri na da kuri'u 150,511 yayin da Sylva ya haɗa kuri'u 91,934, tazarar kuri'u 58,577.

Wace ƙaramar hukuma ce zata yanke hukunci?

A lokacin zaben gwamna na 2019, APC ta samu jimillar kuri’u 124,803 a ƙaramar hukumar Kudancin Ijaw, yayin da PDP ta samu kuri’u 4,098 kaɗai.

Duk da dan takarar APC a zaben gwamna na 2019, Cif David Lyon, ya fito ne daga karamar hukumar Ijaw ta Kudu, amma yankin ya kasance tungar APC tun zaben 2015.

Kara karanta wannan

Zaɓabben Gwamna Usman Ododo ya magantu kan nasararsa a zaɓen Kogi, ya durƙusa a gaban Yahaya Bello

A halin yanzun ana ci gaba da dakon sakamakon zaɓen wannan ƙaramar hukuma da ake ganin ita ce zata zama raba gardama a zaɓen da aka yi ranar Asabar.

Baturen zaɓen jihar Bayelsa, Farfesa Kuta Farouk, shugaban jami'ar tarayya ta Minna a jihar Neja, ya sana% da tafiya hutun karɓan sakamakon zuwa nan da sa'a ɗaya.

Wakilan jam'iyyu sun ba hammata iska a Bayelsa

A wani rahoton kuma Wakilan jam'iyyun APC da Accord sun bai wa hamata iska yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar Bayelsa.

Wakilin jam'iyyar Accord Victor Werinepere-Fisi ya naushi takwaransa na APC, Dakta Dennis Otiotio wamda hakan ya jawo dakatar da shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262