Zaɓen Gwamnan Bayelsa: Timipre Sylva Ya Sake Lallasa Gwamna Diri a Wata Karamar Hukuma
- Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa ya sake lallasa Gwamna Diri na PDP
- Timipre Sylva ya lashe zaɓen ƙaramar hukumar Brass inda nan ne mahaifarsa, inda hakan ya sanya ya lashe ƙananan hukumomi biyu cikin bakwai
- Gwamna Duoye Diri na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yana kan gaba inda ya lashe zaɓen gwamnan a ƙananan hukumomi biyar cikin bakwai
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bayelsa - Timipre Sylva, ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan jihar Bayelsa, ya sake lashe zaɓe a wata ƙaramar hukuma.
Gwamna Duoye Diri na jam’iyyar PDP wanda ke kan gaba a zaɓen ya lashe ƙananan hukumomi biyar.
Amma lokacin da aka dawo tattara sakamakon zaɓen a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, an ayyana Sylva a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a ƙaramar hukumar Brass inda ya fito, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Southern Ijaw kawai ya rage kafin a kammala tattara sakamakon zaɓen.
Ga yadda sakamakon zaɓen na ƙaramar hukumar Brass yake:
Jimillar masu kaɗa ƙuri'a - 94,040
Jimlar masu kaɗa ƙuri'a da aka tantance - 32,064
APC – 18,431
PDP – 12,602
LP - 83
NRM - 31
Ga sakamakon zaɓen sauran ƙananan hukumomin da aka bayyana:
Ogbia
APC - 16,319
PDP - 18,435
LP - 57
Kolokuma-Okokuma
APC - 5,349 PDP - 18,465 LP - 22
SAGBAMA
APC - 6,608
PDP - 35,504
LP - 217
Yenegoa
APC - 14,534
PDP - 37,777
Nembe
APC - 22,248
PDP - 4,556
LP - 113
Ekeremor
APC - 8,445
PDP - 23,172
LP - 50
INEC Ta Ɗage Tattara Sakamakon Zaɓe
A wani labarin da mu ka kawo muku a baya, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ɗage tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Bayelsa na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen ne bayan ta karɓi sakamakon zaɓen gwamnan daga ƙananan hukumomi uku.
Asali: Legit.ng