Gwamnatin Imo Ta Bayyana Dalilin da Ya Sanya PDP, LP Suka Sha Kaye a Zaɓen Gwamnan Imo

Gwamnatin Imo Ta Bayyana Dalilin da Ya Sanya PDP, LP Suka Sha Kaye a Zaɓen Gwamnan Imo

  • Gwamnatin jihar Imo ta yi magana kan nasarar da Gwamna Hope Uzodinma ya samu a zaɓen gwamnan jihar
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya bayyana cew ko kaɗan ƴan adawa ba su shirya sosai kan zaɓen gwamnan ba
  • Declan Emelumba ya yi nuni da cewa rikicin cikin gidan da jam'iyyun adawa ke fama da shi ya sanya suka sha kashi a zaɓen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Gwamnatin jihar Imo ta ɗora alhakin rashin nasarar da jam'iyyun Labour Party da PDP suka yi a zaɓen gwamna da aka kammala a kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye su.

A ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba ne dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana ɗan takarar gwamnan APC kuma gwamna mai ci, Hope Uzodinma, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar na ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zaɓabben Gwamna Usman Ododo ya magantu kan nasararsa a zaɓen Kogi, ya durƙusa a gaban Yahaya Bello

An bayyana dalilin rashin nasarar PDP, LP a zaɓen gwamnan Imo
Gwamnatin Imo ta yi nuni da cewa jam'iyyun adawa ba su shirya wa zaɓen gwamnan Imo ba Hoto: Samuel Nnaemeka Anyanwu, Hope Uzodimma, Senator Athan Nneji Achonu
Asali: Facebook

Ɗan takarar na jam'iyyar APC ya samu ƙuri’u 540,308 inda ya kayar da abokan hamayyarsa na jam'iyyar PDP Samuel Anyanwu wanda ya samu ƙuri’u 71,503 da kuma Athan Achonu na LP wanda ya samu ƙuri'u 64,081.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa PDP, LP suka yi rashin nasara?

Kwana ɗaya bayan nasarar Uzodinma, kwamishinan Yaɗa labarai na jihar, Declan Emelumba, a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels tv, ya ce jam’iyyun adawa ba su shirya wa zaɓen gwamnan ba.

Ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda jam'iyyun biyu suka samu ƙuri'un da suka samu duk da rikicin cikin gida da su ke fama da shi.

A kalamansa:

"Kafin wannan zabe, duk wani mai lura da hankali zai ga cewa kusan ɗaukacin jihar Imo sun fantsama a APC. Jam’iyyar APC ita ce kadai jam’iyyar da ba ta rabe biyu ba, babu sauya sheƙa, babu rikici."

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamnan Bayelsa: Cikakken jerin ƙananan hukumomin da PDP, APC suka lashe ya zuwa yanzu

"Kowace jam’iyyar da ta tsaya takara a wannan zaɓe, tana da rikicin cikin gida, matsalolin cikin gida, ficewar ƴan jam'iyya da dama. Don haka babu yadda za a yi su yi nasara. Babu yadda za a yi su samu ƙuri'un da suka fi waɗanda suka samu."
"Na yi mamakin yadda suka yi nasarar samun ƙuri'un da suka samu domin ba su shirya wa zaɓen nan ba. Ba su yi yaƙin neman zaɓe ba, mutane na ta dawowa daga rakiyarsu."

Jam'iyyun PDP, LP Sun Yi Kiran a Soke Zaɓen Imo

A wani labarin kuma, jam'iyyun Peoples Democraric Party (PDP) da Labour Party (LP) sun yi kiran da aka soke zaɓen gwamnan jihar Imo

Jam'iyyun adawan sun bayyana cewa an tafƙa gagarumin maguɗin zaɓe a zaɓen tare da taimakon jami'a. Tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng