Zaɓabben Gwamna Usman Ododo Ya Magantu Kan Nasararsa a Zaɓen Kogi, Ya Durƙusa a Gaban Yahaya Bello

Zaɓabben Gwamna Usman Ododo Ya Magantu Kan Nasararsa a Zaɓen Kogi, Ya Durƙusa a Gaban Yahaya Bello

  • An gudanar da zaɓen gwamnan jihar Kogi na shekarar 2023 a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023, domin zaɓen sabon gwamna
  • Gwamnan jam'iyyar APC mai ci Alhaji Yahaya Bello ya kusa kammala wa'adinsa kuma ba zai iya sake tsayawa takara a karo na uku ba
  • Sai dai, yaronsa a siyasance Ahmed Usman Ododo ya yi nasara a zaɓen kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana a ranar Lahadi 12 ga watan Nuwamba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Lokoja, jihar Kogi - Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ya yi godiya ga Allah bisa nasarar da ya samu a zaɓe.

Da yake sanya bidiyon daidai lokacin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi na 2023, Ododo ya yi addu’ar Allah ya albarkaci jihar Kogi da Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamnan Bayelsa: Cikakken jerin ƙananan hukumomin da PDP, APC suka lashe ya zuwa yanzu

Ododo ya durƙusa a gaban Yahaya Bello
Usman Ododo ya durƙusa a gaban Gwamna Yahaya Bello bayan nasararsa a zaɓe Hoto: @OfficialOAU
Asali: Twitter

Me Ododo ya yi bayan lashe zaɓe?

Ododo ya rubuta hakan ne a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, tare da sanya wani faifan bidiyo mai tsawon minti ɗaya da daƙiƙa 24.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Alhamdullilah! "
"Dukkan tsarki ya tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki.
"Allah ya albarkaci jihar Kogi!
"Allah ya albarkaci tarayyar Najeriya."

A cikin bidiyon, magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ke a wajen sun taya shi murna yayin da yake nuna godiyarsa ga mai gidansa, Gwamna Yahaya Bello.

Zaɓaɓɓen gwamnan ya durƙusa ƙasa domin nuna godiyarsa ga Gwamna Bello, yayin da gwamnan ya shafa masa kai.

Ododo, wanda tsohon babban mai binciken kuɗi ne kan ƙananan hukumomi a jihar Kogi a ƙarƙashin Bello, shi ne zaɓaɓɓen ɗan takarar gwamnan da ke kawo ƙarshen wa'adinsa na biyu na shekara takwas.

Kara karanta wannan

Zaɓen Kogi: Hadimin Atiku Ya Caccaki INEC, Ya Bayyana Dalilansa

Za a Sake Zaɓe a Kogi

A wani labarin kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana lokacin da za a sake zaɓen gwamnan Kogi, a mazaɓun da aka dakatar da zaɓensu.

A cikin wata sanarwa da hukumar zaɓen ta fitar, ta bayyana cewa za a sake zaɓen ne a ranar, 18 ga watan Nuwamba a wuraren da lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel