Labari Mai Zafi: SDP Ta Doke APC a Karamar Hukumar Farko da INEC ta Sanar a Kogi
Kogi - Murtala Yakubu Ajaka wanda yake rike da tutar Social Democratic Party (SDP) ya shiga zaben jihar Kogi da kafar dama.
A sakamakon zaben farko da hukumar zabe na kasa watau INEC ta sanar, jam’iyyar SDP ce ta yi galaba a zaben Gwamnan Kogi.
Murtala Yakubu Ajaka ne ya fara samun nasara a kan Ahmad Usman Ododo da Dino Melaye a wajen takarar kujerar Gwamna.
Ga yadda sakamakon zaben ya fito kamar yadda labari ya iso mana inda ake da mutane 64,339 da aka yi wa rajista a 2023.
Daga ciki an tantance mutane 23, 044 da za su su kada kuri’a a zaben sabon Gwamnan.
Karamar hukumar Idu
APC: 2,033
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP: 271
SDP: 22,742
Rahotonmu ya nuna an yi watsi da kuri’u 280 daga cikin 23, 022 da aka kada a zaben.
Sai dai sakamakon zaben da su ke fitowa daga baya daga sauran kananan hukumomi sun nuna APC tana shan gaban SDP da PDP.
Asali: Legit.ng