Abubuwa 7 da Su ka Taimaki APC, Suka Kashe LP da PDP a Zaben Gwamnan Imo

Abubuwa 7 da Su ka Taimaki APC, Suka Kashe LP da PDP a Zaben Gwamnan Imo

  • An yi zabe a jihar Imo, kuma Gwamna mai-ci ne ya saje yin nasarar zarce a kan mulki na wasu shekaru hudu
  • Gwamna Hope Uzodinma ya casa jam’iyyar PDP da LP a duka kananan hukumomin da ake da su a Imo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Rahoton nan ya yi duba ga abubuwan da su ka taimakawa APC wajen nasara a zaben Imo:

'Dan takaran Imo
Gwamnan Imo, Hope Uzodinma (APC) Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

1. Karfin mulki

Shugaban da yake kan mulki ya fi samun damar lashe zabe a siyasar Najeriya saboda karfin iko, hukumomi da kuma kudin gwamnati da ke karkashinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu hasashen suna ganin wannan ya yi tasiri mai karfi a zaben Gwamna Hope Uzodinma.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: SDP na bugawa da APC a Kogi, PDP tayi gaba a Bayelsa, APC a Imo

2. Jam’iyyar APC

Baya ga mulkin jiha, APC ke rike da shugabancin kasa kuma tana da rinjaye a duka majalisu, sannan Uzodinma shi ne mataimakin shugaban gwamnonin APC.

Wani abin da ya taimaki jam’iyyar APC shi ne babu rikicin cikin gida sosai reshen Imo.

3. Rigimar cikin gida a PDP

A yayin da ake cewa babu baraka a APC, lamarin ya sha bam-bam a PDP, jam’iyyar hamayyar ta samu rabuwar kai da aka ba Samuel Anyawu takara.

Mutane sun yi tunanin tsohon Gwamna, Emeke Ihedioha zai samu tikiti, hakan ba ta faru ba.

4. Sauya-sheka zuwa APC

Lamarin PDP ba a rikicin gida ya tsaya kurum ba, a lokacin da jam’iyyar ta ke neman goyo baya, sai wasu shugabanni da jagororinta su ka tsallaka zuwa APC.

Irinsu Martins Ejiogu da Ray Emeana sun ragewa PDP karfi da su ka sauya-sheka kwanaki.

5. Raba kan ‘yan adawa

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: DSS da EFCC Sun Dura Rumfar da Dino Melaye Zai Dangwala Kuri’a

Legit ta na tunanin fitowar Anyanwu da Lincoln Ogunewe daga Imo ta gabas ya karfafawa Gwamna mai-ci wajen zarcewa, hakan ya raba kuri’un Owerri.

Sakamakon zaben ya nuna APC ta samu nasara har a garuruwan Ikeduru da Ezinihitte-Mbaise.

6. Yawan mutanen yankin Gwamna

Yankin Imo ta yamma da Uzodinma ya fito na da kananan hukumomi 12, akasin yankunan da manyan ‘yan takaran masu kananan hukumomi tara.

Yawan al’ummar da ke yammacin Imo sun ba APC kwarin gwiwa a zaben gwamnan.

7. Rashin farin jinin Anyawu

Wani matashi ‘dan asalin jihar Imo ya fada mana cewa Samuel Anyawu bai da farin jini wajen jama’a, ya samu tikiti PDP ne saboda sabanin Atiku-Wike.

A cewarsa, a ragowar ‘yan takaran babu wani kwakkwaran ‘dan siyasa da zai ja da APC a Imo.

Sayen kuri'u ya yi aiki a zaben Gwamna

Ku na da labari Hukumar EFCC ta kama mutane 14 dauke da N11m da ake zargi za ayi amfani da su a sayen kuri’u a garuruwan da ake zaben gwamna.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya ce sun karbe N9.3m a Bayelsa da N1.7m a jihar Imo, kuma za a maka wadanda aka kama a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel