Zaɓen gwamnan Imo: Jam'iyyun LP, PDP Sun Yi Kiran da a Soke Zaɓe, Sun Bayyana Dalilansu

Zaɓen gwamnan Imo: Jam'iyyun LP, PDP Sun Yi Kiran da a Soke Zaɓe, Sun Bayyana Dalilansu

  • Ƴan takarar gwamnan jam'iyyun PDP da Labour Party sun yi kiran da a soke zaɓen gwamnan jihar Imo
  • Ƴan takarar sun koka da cewa ba a gudanar da zaɓe ba a jihar maguɗi kawai jam'iyyar APC da INEC suka shirya
  • Sun nuna damuwarsu kan yadda jami'an tsaro suka bayar da haɗin kai wajen yin maguɗin zaɓe a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Jam’iyyar Labour Party (LP) da jam’iyyar PDP sun yi kiran da a soke zaɓen gwamnan jihar Imo da aka gudanar ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar LP, Tony Nwulu, ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a daren ranar Asabar, inda ya ce jami’an tsaro sun bayar da kariya ga wasu mutane yayin da suke murguɗe zaɓen, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Zaɓen Kogi: Hadimin Atiku Ya Caccaki INEC, Ya Bayyana Dalilansa

Anyanwu da Achono sun nemi a soke zaɓen Imo
Yan takarar gwamnan LP, PDP sun nemi a soke zaɓen gwamnan jihar Imo Hoto: Samuel Anyanwu, Athan Achonu
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa jam'iyyar LP ta yi nasara da ainihin ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen, yana mai cewa "dimokuraɗiyya na fuskantar barazana a wannan jihar."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa su ke son a soke zaɓen?

A kalamansa:

"Ba a yi zaɓe a jihar Imo ranar Asabar ba. Abin da ya faru shi ne karkatar da kayan zaɓen zuwa gidajen mutane da kuma hedikwatar ƙananan hukumomi. A duk wannan, ƴan sanda, sojoji da DSS sun ba da tsaro ga masu aikata hakan."
"Sun zo da maƙudan kuɗaɗe zuwa rumfunan zaɓe domin sayen ƙuri’u amma mutanen Imo sun ƙi amincewa da su. A yanzu sun koma ƙwace kayan zaɓe, da karkatar da kayan zaɓe zuwa gidajen mutane da kuma hedikwatar ƙananan hukumomi inda a halin yanzu suke sake rubuta sakamakon zaɓen."
"Muna da dukkanin bayanan. Muna sanar da ƴan Najeriya cewa ba a yi zaɓe a jihar Imo ranar Asabar ba."

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: Ɗan takarar Gwamnan PDP ya lashe rumfar zaɓensa, sakamako ya fito

Matsayin jam’iyyar mu da kuma shugabana, Sanata Athan Achonu, wanda shi ne ɗan takarar gwamna a jam’iyyar shi ne a soke wannan abun kunyan da aka kira zaɓe."

Da yake yiwa manema labarai jawabi a wani taron manema labarai na daban, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Samuel Anyanwu, ya yi kira da a soke zaɓen.

Ya ce INEC da jami’an tsaro sun gaza wajen gudanar da aikin da tsarin mulki ya rataya a wuyansu na gudanar da sahihin zaɓe ga al’ummar jihar.

Ya ce a maimakon haka, jami'an tsaro sun ba wa ma’aikatan INEC kariya yayin da ƴan jam’iyyar APC ke sake rubuta sakamakon zaɓen

Anyanwu ya ce shi da jam'iyyarsa ta PDP ba za su amince da wani abu da ya wuce soke zaɓen baki ɗaya ba.

An Ba Hammata Iska.Wajen Tattara Sakamakon Zaɓe

A wani labarin kuma, an ba hammata iska a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Imo da ke birnin Owerri, babban birnin jihar Imo.

Rikicin ya ɓarƙe ne a tsakanin wakilan jam'iyyu inda aka lakaɗawa wakilin jam'iyyar Labour Party duka tare da yin waje da shi daga wurin tattara sakamakon zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng