Zaben Gwamnan Bayelsa na 2023: Sakamako Zaɓe Daga Kananan Hukumomi Ya Fito, Kai Tsaye
An gama zabe, ana tantance kuri'un kuma an fara kirgawa a wasu rumfunan zabe a jihar Bayelsa inda aka gudanar da zaben gwamna na 2023.
Kasance tare da mu domin samun bayanai kai tsaye dangane da tantancewa da kirga kuri'un da jami'an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ke yi kai tsaye.
Lura: Ku dinga sabunta shafin domin ganin sabbin bayanai.
Ijaw South LGA
APC - 18,174
LP - 119
PDP - 24,685
Masu zabe da suka yi rajista - 184,401
Kuri'u masu kyau - 43,158
Kuri'u marasa kyau - 663
Jimillar kuri'a da aka kada - 43,821
Karamar hukumar Brass
APC - 18,431
LP - 83
PDP - 12,602
Masu zabe da suka yi rajista - 94040
Masu zabe da aka tantance - 32064
An ɗage tattara sakamakon zaɓe sai zuwa Litinin
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da dage tattara sakamakon zaɓen gwammnan jihar Bayelsa, har sai zuwa ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba.
Premium Times ta ce hukumar ta ɗage tattara sakamakon zaɓen ne saboda ƙalubalen da ta fuskanta wajen tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Brass da Southern Ijaw.
Ƙaramar hukumar Ekeremor
APC: 8,445
PDP: 23,172
LP: 50
Ƙaramar hukumar Nembe
Jam'iyyar APC ta samu nasara a ƙaramar hukumar Nembe.
APC: 22,248
PDP: 4,556
LP: 113
Ƙaramar hukumar Sagbama
APC: 6,608
PDP: 35,504
LP: 217
APC ta sake karban kaya a jihar Bayelsa
Timipre Sylva na jam'iyyar APC ya sha kaye a karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa. Gwamna Douye Diri shi ya yi nasara a karamar hukumar da ratar kuri'u fiye da dubu biyu.
Ga yadda sakamakon zaben ya wakana. PDP: 18,435 APC: 16,319.
Karamar hukumar Yenagoa
APC - 14,534
LP - 244
PDP - 37,777
Karamar hukumar Ogbia
ADC - 56 ADP - 45
APC - 16,319 LP - 57 NRM - 37 NNPP - 4 PDP - 18,435
Gwamna Diri na PDP ya lashe ƙaramar hukumarsa
Sakamakon zaɓen karamar hukumar Kolokuma Opokuma.
APC - 5347
LP - 22
PDP - 18,465
NNPP - 22
ADC - 15
ADP -21
Jami'an tsaro sun taka wa masu zanga-zanga birki
Yayin da aka fara tattara sakamakon zaɓen Gwamnan jihar Bayelsa a cibiyar tattara sakamako ta INEC dake Yenagoa, an tsaurara matakan tsaro ta ko ina don aikin ya tafi cikin lumana.
Jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana, sun taka wa masu zanga-zanga na PDP birki, sun hana su shiga ofishin INEC da ke kan titin kasuwar Swali a babbam birni.
Daily Trust ta ce dakaru sun toshe titin da motocin sulƙe da na sintiri.
Sakamakon zaben Bayelsa
Rumfar zaɓe: Sambo I Open Space
Gunduma: Brass ta I
Karamar hukuma: Brass, Bayelsa
APC: 77
PDP: 168
NRM: 3
ZLP: 1
Rumfar zaɓe: Fire Station Open Space
Gunduma: Brass ta II
Ƙaramar hukuma: Brass, jihar Bayelsa
APC: 32
LP: 1
PDP: 72
APM: 1
Rumfar zaɓe: Twon Kubu Community Hall
Gunduma: Brass ta II
Ƙaramar hukuma: Brass, Bayelsa
APC: 72
PDP: 86
Rumfar zaɓe: Makarantar horar da malamai (NTI) Twon Brass
Gunduma: Brass ta II
Ƙaramar hukuma: Brass, Bayelsa
APC: 19
LP: 1
PDP: 29
PRP: 1
Rumfar zaɓe: Makarantar Firamare ta St. Barnabas, Twon
Gunduma: Brass Ward II
Ƙaramar hukuma: Brass, Bayelsa
APC: 19
PDP: 43
Bayelsa 2023: Gwamna Diri ya lashe rumfar zabensa
Akwatin zabe na Sampou/Kalama Ward, PU 004, Kolokuma/Opokuma LG, Bayelsa
APC - 0
ADP - 1
PDP - 218
LP - 0
Zaben gwamnan Bayelsa na 2023: Manyan yan takara
Ga wasu cikin manyan yan takara a zaben gwamnan jihar Bayelsa na 2023 da aka yi ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Alkalluman INEC sun nuna cewa yan takara da jam'iyyun siyasa 16 ne za su fafata a zaben. Sai dai, biyar din da aka jero kasa sune ake yi wa kallon manyan yan takara.
- Douye Diri (PDP)
- Timipre Sylva (APC)
- Udengs Eradiri (Labour Party)
- Waibodei Subiri (APGA)
- Warmate Jones (Accord Party)