Zaben Kogi: Sojoji Sun Tare Hanya, Sun Hana Dan Siyasa da Tawagar Yan Sandan Wuce wa
- Jami'an yan sanda da ke yi wa wani dan siyasa rakiya yayin da ake tsaka da zabe a jihar Kogi sun shiga komadar sojoji
- Jami'an sojin sun tsitsiye yan sandan don jin dalilinsu na fitowa alhalin basa bakin aiki
- Sun ce lallai sai dai yan sandan da dan siyasar su koma inda suka fito kafin daga bisani suka shawo kansu da kyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kogi - An sha yar dirama a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, lokacin da sojoji suka tsayar da jami'an yan sanda da ke yi wa wani dan siyasa rakiya a lokacin zabe, a kauyen Agbadu Bunu da ke karamar hukumar Kaba/Bunu ta jihar Kogi.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, sojoji sun tsayar da ayarin motocin na wasu manyan Jeep uku da wasu kan take dokar takaita zirga-zirgan ababen hawa.
Sojoji sun tsitsiye yan sanda yayin zaben gwamnan Kogi
An tattaro cewa a lokacin da aka tsayar da ayarin motocin, jami'an yan sandan sun je sun samu sojojin yayin da ubangidansu ke hakimce a kujerar baya na Jeep din.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk kokarin da yan sandan suka yi don rokon sojojin ya ci tura yayin da daya daga cikin sojojin ya dauki zafi yana ihun "ba ku aikin zabe. Ku koma!"
Sojan ya tambaya, "Shin ya kamata su (yan sandan) su dunga yawo a yayin zabe? Su je su fada ma ubangidansu ya sauko sannan ya yi wa oganmu bayani. Yau ba ranar da 'babban mutum' zai dunga yawo bane. Gaba daya yan siyasa su tsaya a gidajensu don zuwa kada kuri'a."
Ya dauke su tsawon mintuna 30 kafin sojojin su bar jami'an yan sandan su wuce. A wajen da abun ya faru, an kuma ga wasu manyan motoci da sojojin suka faka.
Sojoji sun kama motoci da ake zargi
A baya mun ji cewa zaben gwamnan jihar Kogi yana da matukar muhimmanci ga al'ummar jihar Kogi masu karamci yayin da mutane suka fara tururuwar fita don sauke hakokinsu, kamar yadda Legit Hausa take bibiya a Arise TV a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
Sai dai a wani yanayi na daban, tawagar rundunar soji na musamman da ke aikin zabe a jihar, ta kama wasu bakaken motocin tsaro guda uku da ba a san daga ina ba, rahoton The Nation.
Asali: Legit.ng