Zaben Jihohi: Gagarumar Matsala Yayin da Aka Fara Siyan Kuri'u N15k, an Bayyana Mazabun
- Matsalar siyan kuri'u ita ke jefa al'umma cikin halin kakani-kayi yayin da ake gudanar da zabe
- A jihar Bayelsa, a yau an samu matsalar siyan kuri'u wurin jama'a masu kada kuri'a a wasu mazabun jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kada kuri'a a jihohin Bayelsa da Kogi da kuma jihar Imo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa - Yayin da ake ci gaba da kada kuri'a a jihar Bayelsa, an fara samun matsalar siyan kuri'u.
Ana zargin an fara siyan kuri'u kan makudan kudade inda mutane ke siyar da 'yancinsu a zaben.
Mene mutane ke korafi a zaben?
TheCable ta tattaro cewa an jiyo wasu na maganan siyan kuri'u a wasu mazabu a birnin Yenagoa da ke jihar Bayelsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zaben na fadin cewa ana siyan kuri'u a mazabar 017 a 'Ward' 10 na karamar hukumar Agudama-Ekpetiama da ke jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jam'iyyar APC na biyan naira dubu 15 yayin da PDP ke biyan dubu 13.
Wace matsala hakan ke jawo wa?
Siyan kuri'u na daga cikin manyan matsaloli da ke kawo cikas a dimukradiyya a Najeriya.
Matsalar siyan kuri'u na kawo cikas a zaben shugabanni nagari yayin da ake gudanar da zabe.
A babban zaben da aka gudanar a watan Faburairu da Maris, an samu irin wadannan matsaloli na siyan kuri'un jama'a.
Asali: Legit.ng