Zaben Imo: Ina da Kwarin Gwiwar Cewa Zan Yi Nasara, Dan Takarar PDP, Anyanwu
- Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Imo, Samuel Anyanwu ya kada kuri'arsa
- Jim kadan bayan ya yi zabe, Anyanwu ya nuna kwarin gwiwar cewa shine zai yi nasara a zaben na yau Asabar, 11 ga watan Nuwamba
- A cewarsa, al'ummar Imo za su zabe shi saboda sun gaji da mulkin zalunci na jam'iyyar APC a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Imo - Samuel Anyanwu, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben jihar Imo, ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa shine zai lashe zaben gwamnan da ke gudana a jihar.
Anyanwu ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a mazaarsa ta makarantar Amaimo, karamar hukumar Ikeduru da ke jihar, a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
Kamar yadda Premium Times ta rahoto, dan takarar na PDP ya ce shine zai lashe zaben saboda mutanen jihar Imo sun gaji da muguwar gwamnatin APC da muradin samun sauyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Ina da karfin gwiwar yin nasara saboda mutanen jihar Imo sun gaji da lalatacciyar gwamnatin APC.
"Sun gaji da rashin tsaro, talauci da rashin aikin yi. Sun gaji da karairayin APC da farfaganda."
Anyanwu ya ce ya samu rahotanni abun dogaro na sace kuri’u a wasu wuraren amma ya dage cewa ko me gwamnati za ta yi, shine zai yi nasara.
Ya ce:
"Ban taba faduwa a zabe ba, akalla na yi takara har sau biyar, zan sake lashe wannan."
Baya ga Anyanwu, sauran manyan yan takara a zaben sun hada da gwamna mai ci, Hope Uzodimma, na APC da Athan Achonu na Labour Party.
Wanene Samuel Anyanwu?
Sanata Samuel Anyanwu, ya kasance fitaccen jigo ne a siyasar Najeriya, wanda ya shahara wajen jajircewa kan yi wa al’umma hidima da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban jama'arsa.
Gudunmawar da ya bayar a fagen siyasa da na taimakon jama’a, na nuni da yadda ya ke da himma wajen inganta rayuwar al’ummar da ya ke wakilta, wanda hakan ya sa ya yi fice a fagen siyasar Najeriya, musamman a jihar da ya fito.
Asali: Legit.ng