Kogi 2023: Ana Tsaka da Kada Kuri'a, An Samu Bullar Sakamakon Zabe, INEC Ta Magantu

Kogi 2023: Ana Tsaka da Kada Kuri'a, An Samu Bullar Sakamakon Zabe, INEC Ta Magantu

  • Rahotanni sun kawo cewa an samu bullar sakamakon zabe yayin da ake tsaka da kada kuri'u a jihar Kogi
  • Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta magantu a kan al'amarin
  • INEC ta ce manyan jami'anta da aka tura yankin suna kan gudanar da bincike domin yi wa tufkar hanci

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ce tana sane da gano bullar takardun sakamakon zabe da aka cika a wasu rumfunan zabe a zaben gwamna da ke gudana a jihar Kogi.

A yau Asabar, 11 ga watan Nuwamba ne al'ummar jihar Kogi ke kada kuri'unsu domin zaben sabon gwamna.

Hukumar INEC ta fara bincike kan zargin bullar sakamakon zabe a Kogi
Kogi 2023: Ana Tsaka da Kada Kuri'a, An Samu Bullar Sakamakon Zabe, INEC Ta Magantu Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar a dandalinta na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya, ta ce an ja hankalinta zuwa ga wani rahoto da ke nuna an samu bullar sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo 2023: 'Yan sanda sun yi arangama da wakilan jam’iyya, an yi harbe-harbe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, hukumar INEC ta tabbatar da cewar ta dauki lamarin da muhimmanci kuma za ta dauki mataki a kai.

Hukumar zaben ta kuma bayyana cewa manyan jami'anta da aka tura jihar suna gudanar da bincike a kan lamarin domin gano bakin zaren.

Ta rubuta a shafin nata:

"Labari da duminsa. An ja hankalin mu zuwa ga wani rahoto da ke cewa an gano takardar sakamakon zabe da aka cika a wasu rumfunan zabe a jihar Kogi.
"Hukumar na bisa kan wannan lamari da gaske.
"A halin yanzu manyan jami’an mu da aka tura jihar suna gudanar da bincike kan lamarin. Hukumar za ta sanar da shawarar da ta yanke."

Dino ya yi zargin magudi a zaben Kogi

Hakan na zuwa ne bayan dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya shaida wa wakilan jam’iyyarsa da su yi turjiya tare da yin zanga-zanga matukar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ki nuna masu tsaftatacciyar takardar rubuta sakamakon zabe.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun damke wasu motoci 3 da ake zargi a zaben jihar Kogi

Melaye, ya ce ba a fara kada kuri’a a Ogori Mangogo ba, saboda ma’aikatan INEC sun ki nuna takardar rubuta sakamakon zabe ga wakilan PDP.

Tsohon dan majalisar, ya bayyana hakan a shafin na X (wanda aka fi sani da Twitter) @_dinomelaye, a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng