Bayelsa: "Dole a Dakatar da Zaɓukan da Ake Yi Ba Tare da Babban Zabe Ba" Tsohon Shugaban Ƙasa
- Goodluck Jonathan ya bukaci majalisar tarayya ta yi aikin gyara zaɓukan Imo, Kogi, Bayelsa da sauransu su koma rana ɗaya da babban zaɓe
- Tsohon shugaban ƙasar ya ce waɗannan zaɓukan da ake yi bayan zaɓen gama gari sun saɓa wa tsarin zaɓe a duniya
- Ya faɗi haka ne jim kadan bayan kaɗa kuri'a a zaben Gwamnan jihar Bayelsa da ake yi yau Asabar, 11 ga watan Nuwamba
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Tsohon Shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya yi kira ga majalisar tarayya da ta fara aikin yadda za a dakatar da zaɓukan da ake yi ba tare da babban zaɓen ƙasa ba.
Jontahan ya yi wannan kira ne bayan ya kaɗa kuri'arsa a rumfar zaɓe ta 39, gunduma ta 13, Otuoke da ke ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa ranar Asabar.
A yau ake gudanar da zaɓukan Gwamnoni a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa wanda ana yinsa ne ba lokaci ɗaya da babban zaɓen ƙasa ba, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na damu matuƙa da zabukan da ake shiryawa daban da babban zaɓen gama gari a ƙasar nan saboda bai dace da mafi kyaun zabukan duniya ba," in ji shi.
Idan baku manta ba a watan Maris da ya gabata aka yi zaɓen Gwamnoni a jihohi 28 cikin 36 da muke da su a faɗin ƙasar nan.
Hakan ta faru ne saboda zaɓukan Gwamnoni a jihohi takwas, Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Kogi, Osun da kuma Ondo, ana yinsu ne bayan babban zaɓe saboda hukuncin Kotu.
Jonathan ya nemi a haɗa zabukan rana ɗaya da babban zaɓe
Amma Jonathan, wanda ya shugabanci Najeriya tsakanin 2010 zuwa 2015, ya ce ya kamata a sauya waɗan nan zabukan da akeyi daban, a haɗa su da babban zaɓe na ƙasa.
A rahoton Channels tv, sohon shugaban ƙasan ya ce:
"Idan muka ci gaba da zaɓuka a lokaci daban da zaɓen gama gari saboda wasu dokoki da ɓangaren shari'a ya yi, wata rana zamu wayi gari shi kansa zaɓen shugaban ƙasa zai zama a lokaci daban."
Ɗan majalisa ya ce zasu binciki Tinubu
A wani rahoton kuma Ɗan majalisar tarayya na APC, Yusuf Gadgi, ya ce zasu tambayi Tinubu abin da aka yi da makudan kuɗin tallafin Fetur da ya cire.
Ya ce yana goyon bayan cire tallafi amma akwai lokacin da zasu gurfanar da Gwamnati ta yi bayanin yadda kuɗin tallafin suka amfani talaka.
Asali: Legit.ng