Rikici Ya Ɓarke Wajen Zaɓe a Bayelsa Yayin da Jami'an INEC Suka Nemi Tsira da Ransu, Bidiyo Ya Fito

Rikici Ya Ɓarke Wajen Zaɓe a Bayelsa Yayin da Jami'an INEC Suka Nemi Tsira da Ransu, Bidiyo Ya Fito

  • An samu rahoton ɓarkewar rikici tsakanin matasa a ƙauyen Agudama-Ekpetiama yayin da ake shirin fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar
  • Rikicin dai ya ɓarke ne yayin da jami'an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) suke shirin fara gudanar da zaɓe a ƙauyen
  • Ɓarƙewar rikicin ya sanya jami'an na INEC sun tsere cikin kwale-kwale domin tsira da rayukansu daga cikin rikicin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Wani rahoto da ke fitowa ya tabbatar da barkewar rikici a yankin Agudama-Ekpetiama na jihar Bayelsa.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, lokacin da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke kafa tantin su domin fara zaɓe.

Kara karanta wannan

Zaɓen Kogi: Jami’an INEC sun maƙale, sun rasa motocin zuwa rumfunan zaɓe, hotuna sun bayyana

Rikici ya ɓarke a Bayelsa
Jami'an INEC sun gudu bayan ɓarkewar rikici a wani ƙauyen Bayelsa Hoto: Twitter
Asali: UGC

Sai dai a lokacin da faɗa ya barke tsakanin matasan yankin, jami’an INEC sun yi sauri sun koma cikin kwale-kwalen su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne dai yayin da ake cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

Menene ya haifar da rikicin?

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a san abin da ya haifar da rikicin ba, sai dai, wannan mummunan lamari, zai shafi fitowar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan da ke gudana a ranar 11 ga watan Nuwamba, a tsakanin mutanen ƙauyen.

A halin da ake ciki kuma, takarar gwamnan jihar Bayelsa tana tsakanin Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP mai neman tazarce inda zai fafata da wasu ƴan takara 15 da suka haɗa da Timipre Sylva na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Udengs Eradiri na jam'iyyar Labour (LP).

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun damke wasu motoci 3 da ake zargi a zaben jihar Kogi

Shugabannin LP sun sauya sheƙa a Bayelsa

A yayin da ake cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa, ɗan takarar zaɓen gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP) Udengs Eradiri, ya samu koma baya ana jajibirin zaɓe.

Wasu shugabannin jam'iyyar na ƙananan hukumomi shida sun juya wa Udengs Eradiri baya, inda suka ce sun dauki matakin ne saboda tsame su da shugabancin LP ta yi daga tsarin yaƙin neman zaɓen gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng