Pdp Ta Gabatar Da Babban Bukata Bayan Batar Kayan Zabe a Hatsarin Jirgin Ruwan Bayelsa
Yenagoa, Jihar Bayelsa - Babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, Peoples Democratic Party, PDP, ta bukaci a maye gurbin kayayyakin zabe da suka bace a hatsarin jirgin ruwa da ya faru a jihar Bayelsa.
Jam'iyyar ta PDP ta gabatar da wannan bukatar ne cikin wani gajeren sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba. An wallafa sanarwar a shafin jam'iyyar na kafar X.
"A kai kayan zabe Koluama": PDP ta fada wa INEC
Idan za a iya tunawa jami'an hukumar zabe 12 sun tsallake rijiya da baya lokacin da jirgin ruwa da ke dauke da su zuwa Koluama a karamar hukumar Kudancin Ijaw ya kife a daren ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardun rubuta sakamakon zabe, na'urar caji, da jakunna dauke da kayan zabe da wasu kayayyakin jami'an na INEC duk sun salwanta.
A martaninta kan afkuwar lamarin, jam'iyyar PDP ta bukaci Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) kada ta tauye wa mutanen yankin hakkinsu na yin zabe.
Sanarwar na PDP ya ce:
"Hukumar Zabe na Kasa mai Zaman Kanta (INEC) @inecnigeria ta tabbatar cewa ba a tauye wa mutanen Koluama da ke Karamar Hukumar Kudancin Ijaw na Jihar Bayelsa hakkin kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Bayelsa ba saboda bacewar kayan zabe a ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamban 2023, a hatsarin jirgi.
"INEC ta tabbatar cewa an sake turawa mutanen kayan zabe a kan lokaci zuwa Koluama."
Kazalika, jam'iyyar ta ce "za ta cigaba da sa ido domin tabbatar da ingantaccen zabe a Jihar Bayelsa".
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng