Zaben Gwamna Na 2023: Muhimman Abubuwa 5 Game Da Siyasar Jihar Imo

Zaben Gwamna Na 2023: Muhimman Abubuwa 5 Game Da Siyasar Jihar Imo

Jihar Imo, Owerri - Imo da ake yi wa lakabi da 'Zuciyar Kudancin Najeriya' na daya cikin jihohi biyar na Kudu maso Gabashin Najeriya. Tana da kananan hukumomi 27 da kuma yankunan uku.

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Ga wasu muhimman abubuwa na siyasa game da daya cikin tsaffin jihohin Najeriya wato Imo.

Muhimman batutuwa kan siyasar Imo
Zaben gwamna: Gwamnonin farar hula 7 da wasu muhimman batutuwan siyasa game da Imo: Hoto: Hope Uzodimma
Asali: Facebook

Kirkirar Jihar

An kirkir jihar Imo ne a 1976, bayan Yakin Basasan Najeriya a zamanin mulkin Murtala Mohammed, shugaban mulkin soja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kirkiri jihar ne daga tsohuwar Jihar Kudu ta Tsakiya kuma an samo sunan daga Rafin Imo.

A 1991, gwamnatin tarayya ta raba jihar ta kirkiri Abia, kuma wani sashin ya zama jihar Ebonyi a 1996, a cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Kogi: Muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da dan takarar SDP, Murtala Ajaka

Gwamnonin farar hula bakwai da aka zaba

Gwamnonin farar hula bakwai suka mulki jihar tun kirkirar ta.

  • Samuel Onunaka Mbakwe - mamban jam'iyyar Nigerian Peoples Party (NPP) ne da ya mulki jihar daga 1979 zuwa 1983 a Jamhuriya ta Biyu.
  • Evan Enwerem na jam'iyyar National Republican Convention (NRC) ya mulki jihar daga 1992 zuwa 1993 a Jamhuriya ta Uku.
  • Achike Udenwa - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga 1999 - 2007.
  • Ikedi G. Ohakim ya lashe zabe karkashin jam'iyyar Progressive Peoples Alliance (PPA) kuma ya koma PDP. Ya yi gwamna daga 2007 zuwa 2011.
  • Owelle Rochas Anayo Okorocha ya zama gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) amma daga baya ya koma APC. Okorocha ya yi mulki daga 2011 - 2019.
  • Emeka Ihedioha - Gwamnan na PDP bai cika ko shekara daya kan mulki ba kafin Kotun Koli ta Tsige shi ta ayyana Uzodimma a matsayin wanda ya lashe zaben 2019. Ya yi mulki daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa 20 ga watan Janairun 2020.
  • Hope Uzodimma - Dan takarar na APC ya zama gwamna bayan Kotun Koli ta sauke Ihedioha.

Kara karanta wannan

Zaben 11 Ga Nuwamba: Jerin Gwamnonin Jihar Kogi Daga 1999 Zuwa Yanzu

Gwamnonin mulkin soja tara

  • Ndubuisi Kanu
  • Adekunle Lawal
  • Sunday Ajibade
  • Adenihun Ike
  • Nwachukwu Allison
  • Amakoduna Madueke
  • Amadi Ikwechegh
  • Anthony E. Oguguo
  • James N.J. Aneke
  • Tanko Zubairu

Kotu ta sauke gwamna

Kotun Koli ta sauke Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP a ranar 20 ga watan Janairun 2020, kuma ta umurci INEC ta ayyana Uzodimma a matsayin wanda ya lashe zaben 2019.

Zaben gwamna ba tare da sauran jihohi ba

Jihar Imo na daya cikin jihohi bakwai da suke zabe ba tare da sauran jihohi yayin zabe ba.

A ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, mutanen Imo za su fito su kada kuri'a don zaben wanda suke son ya jagorance su na shekaru hudu nan gaba.

Kazalika, gwamnonin Imo biyu sun sauya jam'iyya yayin da suke ofis - Ohakim daga PPA zuwa PDP da Okorocha daga APGA zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Zaben Imo 2023: Jerin sunayen gwamnonin jihar Imo daga 1999 zuwa yanzu

Mace Tilo a Zaben Gwamnan Kogi, Fatima Taiye Suleiman

Ba kasafai mata suka cika samun manyan mukaman siyasa a Najeriya ba duba da yadda maza suka yi wa harkar siyarsa kaka-gida.

Sai dai, duk da hakan a kan samu kallabi cikin mata a wasu zabukan kamar yadda aka samu Fatima Taiye Suleiman a zaben gwamnan jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164