Fatima Taiye Suleiman: Muhimman Abubuwa 5 Kan Ƴar Takarar Gwamna Mace Tilo a Zaben Gwamnan Kogi

Fatima Taiye Suleiman: Muhimman Abubuwa 5 Kan Ƴar Takarar Gwamna Mace Tilo a Zaben Gwamnan Kogi

Lokoja, jihar Kogi - Yanayin siyasar Najeriya baya ba mata kulawa ta musamman saboda haka sai mace mai jajircewa da karfin gwiwa ce kawai za ta iya shiga harkar siyasa.

Mace guda da ta amsa sunan mai kamar maza, kuma bata shayin gwabzawa da takwarorinta maza a siyasa ita ce Hon. Fatima Taiye Suleiman.

Fatima Taiye ita kadai ce mace a cikin yan takarar gwamnan Kogi
Fatima Suleiman: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Yar Takara Mace 1 Tak a Zaben Gwamnan Kogi Hoto: Kogi Reports
Asali: UGC

Gogaggiyar yan siyasar ita ce mace daya tilo da ta tsaya takarar gwamna, inda take wakiltar jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP), a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar Kogi.

Fatima tana da abubuwa masu ban sha'awa da ya kamata a sani game da ita.

Ta kasance haifaffiyar garin Okene a karamar hukumar Okene a yankin Kogi ta tsakiya kamar dai gwamna mai ci, Yahaya Bello.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kogi: Jimami yayin da shahararren dan siyasar APC ya riga mu gidan gaskiya awanni kadan kafin zabe

Tela

Gogaggiyar yar siyasar, wacce aka haifa a jihar Kwara ta kasance shahararriyar tela da ke zama a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Tsohuwar yar PDP

Fatima ta kasance tsohuwar yar jam'iyyar PDP kuma ta yi aiki a nasarar da Sanata Dino Melaye ya samu a Kogi ta yamma a 2015.

Gogaggiyar yar siyasa

Ta bayyana cewa shugaban jam'iyyar ZLP, Dan Nwanyanwu, ne da kansa ya kira ta don ta yi takara a zaben gwamnan.

Ta yi takara a zaben sanata na ranar 25 ga watan Fabrairu, a babban zaben 2023.

Mulkin karba-karba

Fatima ta ce tana goyon bayan mulkin karba-karba amma bata ga wani abu ba idan jam'iyyar APC mai mulki ta gabatar da dan takara daga yankin da gwamna mai ci yake ba.

Ta bar ZLP zuwa APC

Fatima ta sauya sheka daga jam'iyyarta, ZLP saboda dan takarar APC, Usman Ahmed Ododo.

Jam'iyyun siyasa guda biyar ne suka yanke shawara a karkashin jam'iyyar United Progressive Political Parties (UPPP).

Kara karanta wannan

Fitaccen dan takarar gwamnan jihar Kogi ya janye ana dab da zabe? Gaskiya ta bayyana

Jam'iyyun da suka lamuncewa Ododo sune Action Democratic Party (ADP), Action People’s Party (APP), Zenith Labour Party (ZLP), National Rescue Movement (NRM), da Because Of Our Tomorrow (BOOT) party.

Sunayen yan takara 18 a zaben Kogi

A baya Legit Hausa ta kawo cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta tantance jimillar yan takara 18 domin fafatawa a zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar Kogi.

Yan takarar suna fafutuka don karbar mulki daga hannun Gwamna Yahaya Bello mai ci a watan Janairun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng