To Fa: Ana Jajibirin Zaɓe, Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar APC Ya Sha da Kyar

To Fa: Ana Jajibirin Zaɓe, Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar APC Ya Sha da Kyar

  • Ɗan takarar Gwamna a inuwar APC a zaben jihar Bayelsa, Mista Sylva, ya sha da kyar a Kotun ɗaukaka ƙara ana gobe zaɓe
  • Kwamitin alkatan Kotun, ranar Jumu'a, ya yi watsi da sabuwar ƙarar da aka shigar ana neman hana Sylva takara
  • Kotun ta kuma yi fatali da zargin cewa zaben fidda gwanin APC ya saɓa wa tanade-tanaden doka

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka kara mai zama Abuja ta yi watsi da sabuwar karar da aka nemi cire Timipre Sylva, ɗan takarar Gwamna a inuwar APC daga zaben Gwamna ranar Asabar.

Dan takarar Gwamnan APC a zaben Bayelsa, Timipre Sylva.
Zaben Bayelsa: Dan Takarar APC Sylva Ya Sha da Kyar a Jajibirin Zabe Hoto: Timipre Sylva
Asali: Facebook

Kwamitin Kotun mai ƙunshe da alƙalai uku ya yanke cewa ƙarar ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa tsarin doka domin an shigar da ita bayan lokaci ya wuce, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta tanke hukunci kan nasarar ɗan Majalisar Tarayya bayan kotun zaɓe ta tsige shi

A hukuncin da alkalan suka yanke wanda mai Shari'a Binta Zubair ta karanto ranar Jumu'a, Kotun ta amince da tuhumar cewa sau biyu ana rantsar da Sylva a matsayin Gwamnan Bayelsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Ƙotun ta bayyana cewa hakan bai saɓa wa doka ba saboda sahihiyar Kotu ta soke karo na farko da aka rantsar da Sylva a matsayin Gwamna.

Bugu da ƙari, a ƙara mai lamba CA/ABJ/CV/1052/2023, Mai shari'ar Zubar ta yi fatali da ƙorafin cewa zaben fidda gwanin da APC ta yi a watan Afrilu ya saɓa wa tanade-tanaden doka.

Dalilin da ya sa Kotu ta kori ƙarar

Ƙotun ta lura da cewa shaidun da hukumar zabe (INEC) da APC suka gabatar sun nuna cewa an bi dukkan matakan da doka ta tanada wajen gudanar da zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar Gwamanan PDP

Wani mamban jam’iyyar APC, Hon Isikima Ogbomade Johnson ne ya shigar da karar yana kalubalantar zaben fidda gwanin da ya samar da Sylva a matsayin ɗan takara.

Amma Sylva ya ce ya samu kuri'u mafi rinjaye 52,062 inda ya zo na daya, yayin da wanda ya shigar da kara ya zo na hudu da kuri'u 584, The Sun ta ruwaito.

Kotu ta hana ma'aikata shiga yajin aiki

A wani rahoton kuma Ƙungiyoyin kwadago na kasa da sauran kawayensu sun gamu da cikas a yunkurinsu na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Kotun ɗa'ar ma'aikata ta Najeriya ta hana ƙungiyoyin ma'aikatan shiga yajin aikin a wani hukuncin cikin shari'a da ta yanke ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262