Kogi: Dino Melaye Ya Lissafa Jerin Sunayen Yan Siyasa da Ake Son Kashewa

Kogi: Dino Melaye Ya Lissafa Jerin Sunayen Yan Siyasa da Ake Son Kashewa

  • Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa, ya lissafa wasu yan siyasa hudu da ake kokarin kashewa
  • Tsohon sanatan ya yi zargin cewa yan siyasa daga yankin Kogi ta tsakiya sune mutanen da jam'iyyar APC mai mulki ke son kashewa
  • Melaye ya yi kira ga hukumomin tsaro da mutanen jihar da su rike APC idan wani abu ya samu yan siyasar da ya ambata

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna na ranar Asabar, Nuwamba 11 a jihar Kogi, ya ambaci sunayen wasu yan siyasa a jihar da ake kokarin kashewa.

Kara karanta wannan

Zaben 11 Ga Nuwamba: Jerin Gwamnonin Jihar Kogi Daga 1999 Zuwa Yanzu

Tsohon sanatan ya yi zargin cewa wadannan yan siyasa, wadanda ya ambaci sunayensu, sune jam'iyyar APC mai mulki ke kokarin kashewa, inda ya yi kira ga hukumomin tsaro da su lura da kyau.

Sanata Dino Melaye ya yi zargin cewa ana kokarin kashe wasu yan siyasa
Kogi: Dino Melaye Ya Lissafa Jerin Sunayen Yan Siyasa da Ake Son Kashewa Hoto: Senator Dino Melaye
Asali: Instagram

Ya yi zargin cewa yan siyasar da ake son farmaka sun fito ne daga yankin Kogi ta tsakiya, inda ya kara da cewar idan wani abu ya faru da wani daga cikin yan siyasar hudu, toh a rike gwamnatin APC a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Melaye ya zargi APC da kokarin kashe magoya bayansa hudu

Zargin na zuwa ne yan kwanaki kafin zaben, inda Melaye da PDP suka riga suka fara kamfen don karbe mulkin jihar daga hannun APC mai mulki.

An bayyana zaben a matsayin zazzafan takara tsakanin APC mai mulki, PDP da kuma SDP. Yayin da Melaye ke takara a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Usman Ododo yana takara a inuwar APC, yayin da Yakubu Murtala Ajaka ke rike da tutar SDP.

Kara karanta wannan

Zan gina mu ku otal a kan ruwa, dan takarar gwamna a jihar Kogi ya yi alkawari, ya fadi dalili

Sai dai kuma, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta wallafa sunayen yan takara 18 da za su fafata a zaben amma da alama Melaye ne babban abokin hamayyar jam'iyya mai mulki, musamman da nasarar da Sanata Akpoti-Uduaghan ta samu a Kogi ta tsakiya.

Kalli bidiyon zargin a kasa:

APC za ta lashe zaben Kogi - Ayodele

A wani labarin, mun ji cewa Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta lashe zaben gwamna a jihar Kogi, wanda za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Alhaji Ahmed Ododo shine dan takarar jam'iyyar APC, kuma shine dan takarar da gwamna mai ci, Yahaya Bello ke goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng