Zabukan Kogi, Imo, Bayelsa: Malamin Addini Ya Ce APC Za Ta Lashe Jihohi 2, Ya Bayyana Su
- An shirya gudanar da zabukan gwamnoni guda uku a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi
- Za a gudanar da zaben a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba - watanni takwas bayan babban zaben Najeriya
- A wata wallafa da ya yi a Facebook mai taken 'hasashen zabukan gwamnoni da za a yi', Apostle Ako Anthony, ya bayyana abun da ya hango game da jam'iyyun da za su yi nasara
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Lokoja, Jihar Kogi - Apostle Ako Anthony na cocin Mountain of Christ Prayer Ministry International ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC za ta lashe jihohi biyu a zaben da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
A yayin wani shirin kai tsaye a dandalin Facebook a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, wanda jaridar Legit ta gani, Apostle Anthony ya ce babbar jam'iyyar adawa ta PDP za ta lashe zabe a jihar Bayelsa. Gwamna Duoye Diri ne dan takarar PDP a jihar Bayelsa.
Zabukan gwamnoni: "Na hango 2/1", Apostle Anthony
A cewar Apostle Anthony, a jihar Imo, Hope Uzodimma zai kwato kujerarsa ta kowani hali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ce a jihar Kogi, za a ayyana Ahmed Ododo na APC a matsayin wanda ya yi nasara.
Apostle Anthony ya ce:
"Idan za a sanar da jama'a sakamakon, na yarda zai kasance PDP jiha daya, APC, jihohi biyu. Wannan shine abun da nake gani a badini.
"Kuma ba zai zamo abu mai sauki ba ga jam'iyyar adawa ta karbe jiha daya, amma shakka babu jihohi biyu na APC ne. Sai kuma daya jihar, wannan na PDP ne, amma dai gwagwarmaya ne.
Ya ci gaba da cewa:
"Jihar Imo, APC za ta karbe ta kowani hali, APC za ta kwace jihar Kogi, sannan na jihar Bayelsa, za a fafata. PDP za ta fafata don dawo da jihar Bayelsa saboda akwai wani abu da aka shuka a baya.
"Na hango biyu bisa daya a zaben - ba uku da sifili ba.
"Na gama magana, wannan shine abun da na gani ko shakka babu."
Gwamnan Kogi: Ajaka bai janye ba - SDP
A wani labarin, jam'iyyar SDP ta karyata rade-radin cewa dan takararta a zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi, Muritala Yakubu Ajaka, ya janye daga tseren.
Kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto jam'iyyar ta bayyana wannan rahoton a matsayin kanzon kurege, cewa wani abu mai kama da haka bai faru ba.
Asali: Legit.ng